Kungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa ana kashe dala biliyan 1.4 duk shekara wajen kula da matan da aka yi wa kaciya a duniya.
Kungiyar ta fadi haka ne a taron ranar yi wa mata kaciya ta duniya da ake yi duk ranar 6 ga Fabrairu.
WHO ta ce ga dukkan alamu duniya za ta samu kari a kudaden da take kashewa wajen kula da matan da aka yi wa kaciya idan har ba a dauki matakin hana al’adan ba.
Bincike ya nuna cewa an yi wa mata sama da miliyan 200 kaciya a kasashe 30 dake Afrika, Gabad ta Tsakiya da Asia.
WHO na hasashen cewa mata miliyan 4.4 na cikin hadarin a yi musu kaciya a shekarar 2024.
Hakan na nuna cewa mata sama da 12,000 za a yi musu kaciya ya duk rana a duniya.
Illolin yi wa mata kaciya
1. Yawan yin Fushi
2. Tabuwar hankali
3. Rashin son saduwa da Namiji
4. Yakan kawo wahala wurin haihuwa
5. Yoyon fitsari ga ‘Ya mace
6. Mata kan kamu da wasu cuttutuka a gabansu
7. Zuban jini da har ya kan kai ga mutuwa
8. Samun matsala wurin yin fitsari da kuma sauran su.
Kungiyar lafiyar ta ce za ta hada ƙarfi da karfe tare da saka bakin masu ruwa da tsaki a kasashen da wannnan al’ada ya yi wa katutu domin tabbatar da kawo karshen wannan matsala.
Discussion about this post