‘Yan bindiga karkashin jagorancin shahararren dan bindiga Daminan sun kashe mutum 10 a kauyen Kwanar Dutse a jihar Zamfara.
Daminan tare da dakarun sa sun kai wa kauyen hari ranar Laraba da misalin karfe hudu na yamma dalilin kin biyan sa harajin naira miliyan 20 da ya saka musu su biya.
Kauyen Kwanar Dutse dake masarautar Dansadau a karamar hukumar Maru na daga cikin kauyukan dake yawan fama da hare-haren ‘yan bindiga a jihar Zamfara.
Wani mazaunin kauyen ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun shigo kauyen su bayan sallar Ishai.
“Muna zaune muna hira a gaban masallaci sai maharan suka shigo suna harbi ta ko ina, sai dai ‘yan banga sun yi kokarin dakile harin sai dai hakan ai yiwu musu ba saboda karfin makaman ƴan bindigan.
“Na gudu na boye a gida inda a nan ne na samu mafaka.
‘Yan bindiga sun kona wasu gidaje da shaguna a kauyen.
Wani dagace a kauyen ya ce wani dan uwan sa na daga cikin mutanen da maharan suka kashe a kauyen.
Daga nan wani mazaunin kauyen da baya so a fadi sunnan sa saboda tsaro ya ce gidan sa na cike da ‘yan gudun hijira daga Kwanar Dutse.
“Mutane daga kauyukan Malele, Ruwan Tofa, Mutunji da Kwana da mazauna kauyukan Arewacin Dansadau na cikin tsaka mai wuya.
“Maharan na yawan saka wa kauyuka harajin dole sannan idan suka basu iya biya ba sai su shigo su kashe su kamar dabbobi.
Discussion about this post