Femi Adesina, Tsohon Kakakin Yaɗa Labaran Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi watsi da iƙirarin da tsohon Kakakin Yaɗa Labaran Goodluck Jonathan, Ruben Abati ya yi cewa ya sha karo da aljanu da dodanni a cikin Fadar Shugaban Ƙasa a ranar tsakar dare.
Shi kuwa Adesina, cewa ya yi a shekaru takwas da ya shafe ya na kwana cikin Fadar Shugaban Ƙasa, bai taɓa cin karo, hange ko giftawar aljani ko dodanni a fadar ba.
Adesina wanda aka ƙaddamar da littafin da ya wallafa kan rayuwar shekara takwas da ya yi tare da Buhari, ranar Talata a Abuja, ya yi wannan bayani a ranar Talatar gabanin ƙaddamar da littafin a gidan talabijin na Channels.
Adesina ya yi Kakakin Yaɗa Labaran Buhari daga Mayu 2015, zuwa Mayu 2023. Yayin da Garba Shehu ne Babban Hadimin Buhari kan yaɗa labarai.
“Ni dai a tsawon shekaru takwas da na yi cikin Villa, ban ci karo da aljanu ko dodanni ko kambultu ba.” Haka ya faɗa da aka tambaye shi ko ya taɓa cin karo da aljanu ko dodanni ko mayu, kamar yadda Abati ya furta a cikin 2016.
“Ruben ya ce ko sau ɗaya bai taɓa barci a gidan da aka ba shi cikin Villa ba, saboda lokacin da ya fara shiga, ya kwanta kenan sai wuta ta tashi, shi kuma ya fice daga gidan.
“Ni dai shekara ta takwas a cikin Fadar Shugaban Ƙasa, ba ma barci kaɗai ba, har minshari na ke yi. Saboda ni ƙarar minshari na ce ma ke tayar da ni. Hakan ya nuna lafiya ƙalau na ke zaune, ba abin da ke firgita ni.”
Tun da farko a ranar Talata ɗin, Adesina ya ƙaddamar da littafi na shekaru takwas da ya yi ya na aiki tare da Buhari, daga 2015 zuwa 2023.
Taron dai ya damu halartar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Shugaba Bola Tinubu, tsohon Shugaban Mulkin Soja, Yakubu Gowon da wasu manya da dama.
Discussion about this post