Kamfanin mai na NNPCL ya bayyana cewa ya samu ribar da bai taɓa samun irin ta a cikin watanni 16 ba.
NNPCL ya ce bayan ya cire kuɗaɗen haraji ya biya, sauran zunzurutun kuɗi riba da ya samu a cikin watanni 16, sun kai Naira tiriliyan 2.5.
An samu wannan riba da aka bada labari daga watan Satumba, 2021 zuwa Disamba 2022, watanni 16 kenan.
Kamfanin ya ce kuɗaɗen shigar da ya samu za su iya fin haka ba don taguwar man fetur da ake samu ba.
Sai dai kuma NNPCL ya ce a cikin watannin 16 ya kashe Naira tiriliyan 2.4 kan tallafin fetur, wanda Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya soke cikin watan Mayu, a ranar da ya hau mulki.
Kuɗaɗen tallafin da gwamnati ke kashewa kan fetur a zamanin gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya kai kashi 35.8 na adadin yawan kuɗaɗen cinikin fetur ɗin.
NNPCL ya ce ya kashe Naira tiriliyan 1.7 wajen hidimar gudanarwar ayyukan kamfani da ofis na yau da kullum.
Cikin makon nan ne kuma Gwamnatin Tarayya bayyana cewa Hukumar FIRS ta tara harajin Naira tiriliyan 12 cikin 2023, ta ce sai ta tara tiriliyan 19 cikin 2024.
Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Tarayya (FIRS), ta bayyana cewa ta tara har Naira tiriliyan 12.374 a matsayin haraji cikin shekarar 2023.
Wannan adadi dai ya zarce adadin da aka nemi tarawa tun da farko a shekarar, wato Naira tiriliyan 10.7.
Shugaban Hukumar FIRS, Zacch Adedeji ne ya bayyana haka a wani taron da FIRS ta shirya na sanin-makamar-aiki na kwana biyu, a Ɗakin Taron Transcorp Hilton, Abuja.
Taron wanda aka buɗe a ranar Laraba, ya ce Gwamnatin Tarayya ta bai wa FIRS umarnin ta yi dukkan ƙoƙarin da za ta yi domin ganin ta tara haraji na aƙalla Naira tiriliyan 19.4 cikin shekarar nan ta 2024.
Adedeji ya ce FIRS za ta cimma wannan ƙudiri na ganin ta tara Naira tiriliyan 19.4 a 2024 ɗin, tare da yin amfani da kyakkyawan tsarin karɓa da tara kuɗaɗen haraji, tare kuma da samar da dama da masu masana’antu za su yi harkokin su.
A wurin taron, Ministan Harkokin Kuɗaɗe Wale Edun ya jinjina wa Adedeji ganin ya zarce adadin da aka umarce shi ya tara a 2023.
Wata babbar jami’ar FIRS mai suna Amina Ado, ta ce an tara Naira tiriliyan 3.17 daga harajin harkokin fetur, harkokin da ba na fetur ba kuwa an tara Naira tiriliyan 9.2.
Tun da farko dai Naira biliyan 10.7 aka nemi FIRS ta tara.
Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban FIRS, Dare Adekanmbi.
Discussion about this post