Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato, ya yi kira da babbar murya cewa ya dace a yi adalci ga ‘yan majalisar dokoki, na tarayya da sanatocin PDP na Jihar Filato waɗanda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tsige ba bisa ƙa’ida ba.
Gwamnan wanda shi ma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tsige, amma Kotun Ƙoli ta maida shi kan kujerar sa, ya ce tunda shari’ar sa duk irin ɗaya ce da ta ‘yan majalisar PDP da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tsige, to ya kamata a yi gaskiya, a fito a yi masu adalci.
Mutfwang ya yi wannan kira yayin da ya ke wa manema labarai jawabi, lokacin da ya ziyarci Shugaban Hukumar Inganta Manyan Makarantu, TETFund, Sonny Echono, a Abuja.
Gwamnan ya gode wa ‘yan Najeriya da suke ta nuna a yi masu adalci. Kuma ya gode wa waɗanda suka damu har shi ma Kotun Ƙoli ta yi masa adalci, ta maida masa kujerar sa.
Kotun Ɗaukaka dai ta tsige dukkan ‘yan majalisar dokokin PDP na Jihar Filato, su 16, sai kuma na tarayya su 5 da kuma sanatoci 2.
An tsige su ne a kan batu na cikin jam’iyya, rashin bin umarnin kotu da kuma rashin tsari a jam’iyya.
Sai dai kuma dangane da irin wannan zargin kan Gwamna Mutfwang, Kotun Ɗaukaka Ƙara shi ma ta tsige shi, amma kuma Kotun Ƙoli ta maida shi.
Inda maganar ta ke a nan shi ne su sanatoci da ‘yan majalisa, ba su da hurumin ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli, kamar yadda shi gwamna ya yi.
Discussion about this post