Matatar Ɗanyen Mai ta Ɗangote wadda ta fara tace ɗanyen mai kwanan nan da ke Legas, za ta shigo da ɗanyen mai daga Amurka nan ba da daɗewa ba, kamar yadda wani rahoto ya tabbatar da hakan.
Kanfanin Trafigura ya saida wa Matatar Ɗangote ganga miliyan 2 ta ɗanyen mai samfurin WTI Midland, wanda za a lodo shi a cikin watan Fabrairu, kamar yadda jaridar Blooberg ta ruwaito a ranar Litinin.
Jaridar ta ji wannan bayani ne daga wata majiyar da ke da masaniya kan cinikin.
Wannan ne karon farko da Matatar Ɗangote za ta sayo ɗanyen mai daga wata ƙasa wajen Najeriya.
A farkon watan Janairu dai Matatar Ɗangote ta fara tace dizal da man jiragen sama.
A farkon fara tacewa, masana’antar ta ce ta karɓi gangar ɗanyen mai miliyan 6 daga Shell International Trading and Shipping Company Limited (STASCO).
An sauke lodin farko a ranar 12 ga Disamba, 2023, zai kuma 6 ga da 8 ga Janairu.
Za a iya loda tankar man fetur 2,900 kowace rana daga Matatar Man Ɗangote.
Yayin da Matatar Ɗangote ta fara aiki, su dai ‘yan Najeriya da dama na fatan za a samu sauƙi da rangwamen farashin litar fetur, wanda yanzu lita ɗaya ta haura Naira 600, tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin fetur.
Discussion about this post