Najeriya ta nuna damuwa da rashin jin daɗin yadda ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso suka fice daga ƙungiyar ECOWAS.
A ƙarshen makon jiya ne dai ƙasashen uku suka bayyana ficewar su, bisa zargin cewa ƙungiyar ta kauce daga bin turbar da magabatan da suka kafa ta suka ɗora ta a kai.
Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, mai suna Francisca Omayuli ta sa wa hannu a ranar Litinin, ta ce ECOWAS ta yi aiki tuƙuru wajen samar da zaman lafiya, ƙaruwar arziki da inganta dimokraɗiyya a Afrika ta Yamma.
“Najeriya ta na nan kan bakan ta na goyon bayan ECOWAS da kuma bin ƙa’idoji da ƙoƙarin kare ‘yan ƙasashen da ke cikin ƙungiyar.” Cewar sanarwar.
Sai dai kuma ECOWAS ta ce ƙasashen uku ba su bi ƙa’idojin da ECOWAS ta gindiya wa duk ƙasar da ke neman ficewa daga ƙungiyar ba.
A ranar Lahadi ce Nijar, Mali da Burkina Faso suka bayyana ficewar su daga ECOWAS.
Ƙasashen Mali, Nijar da Burkina Faso sun bayyana ficewar su daga Ƙungiyar Ƙasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS.
Ƙasashen uku dai su na ƙarƙashin mulkin soja ne, bayan juyin mulkin da ya hamɓarar da shugabannin fararen hula a ƙasashen, inda Nijar ce ta baya-bayan nan.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito Shugabannin ƙasashen uku sun zargi ECOWAS da rashin tausayin bil-Adama, biyo bayan takunkumin da aka ƙaƙaba masu.
Cikin wata sanarwar haɗin-guiwa da suka fitar, wadda aka aka watsa a gidajen talbijin na ƙasashen uku, sun ce “mun yanke shawarar tsayawa da ƙafafuwan mu, bisa doron ‘yancin mu. Don haka mun ayyana ficewar mu daga ECOWAS, saboda ƙungiyar ta kauce daga bin kyawawan manufofin da waɗanda suka kafa ta suka ɗora ta a kai, bayan shekaru kusan 50 da kafuwar ta.
“Haka kuma ECOWAS ta bi son ran wasu ƙasashen Turai, har ƙungiyar ta zama barazana ga ɗimbin al’ummar mambobin ƙasashen ta, waɗanda aka kafa ta domin ta faranta masu, ba don ta faranta wa Turawan Yamma ba.”
Ƙasashen sun fice ne bayan watannin da aka ɗauka ana kwan-gaba-kwan-baya don ganin an dawo da mulkin farar hula a ƙasashen uku.
ECOWAS ta ƙaƙaba masu takunkumi kuma har yanzu kan iyakokin Najeriya da Nijar a rufe su ke, kuma an yanke wutar lantarki daga Najeriya zuwa Nijar.
An dai shirya yin taron Ministocin Harkokin Wajen ECOWAS a Yamai, babban birnin Jamhuriyar a ranar 25 ga Janairu, amma abin bai yiwu ba.
“Tawagar ECOWAS ta yini cur a filin jirgin saman Abuja zuwa Nijar, amma daga baya aka sanar cewa “jirgin da zai ɗauke su ya samu matsala.”
Discussion about this post