Ƙasar Angola ta yi wa ‘yan wasan ta albishir da alƙawarin kyautar miliyan 5 Ga kowane ɗan wasa muddin suka doke Najeriya.
Angola za ta ba kowanen su Kwanza miliyan 5 kamar yadda ake kiran kuɗin ƙasar.
Haka shi ma kamfanin wayoyin sadarwa na UNITEL na ƙasar ya yi wa kowanen su alƙawarin waya ƙirar iPhone 15 idan su ka yi galaba kan Najeriya, a wasan na kusa da na ƙarshe, wato ‘quater final’ da za su kara.
Najeriya ta caskara Kamaru da ci 2:0, inda za ta kara da Angola a wasa na gaba.
Idan Angola ta yi galaba kan Najeriya, zai kasance karo na farko da ƙasar ta taɓa kaiwa wasan kusa da na ƙarshe, wato ‘semi final’.
Gasar AFCON dai ta ɗauki zafi yayin da aka yi waje rod da masu riƙe da kofi, wato Senegal tun a wasan zagaye na biyu.
Discussion about this post