Rikicin Sadiya Marshal da Layla Othman, ya dau sabon salo, yayin da mijin Layla Honarabul Yusuf Gagdi ya yi barazanar ɗaure Sadiya Marshal a kurkukun Kuje.
Tun bayan sakin wani bidiyo da Marshal ta yi in da ta zargi Layla da yi mata ƙazafi da kuma kiranta masifaffiya ta fito ta yi barazanar fallasa wasu bidiyo da hotunan da ta ke da su game da abubuwan da Layla take yi a boye.
Ta zargi Layla da yin mu’amula da maza bayan ta na da aure.
” Ina da faifai abinda kike yi kuma idan kika ja daga da ni zan fallasa ki kowa ya san abubuwan da kike yi a boye.
Mashal dai ta rika zaro maganganu ta inda take hawa ba ta nan ta ke sauka ba.
” An gaya miki ba mu san inda kike samun kuɗi bane. Wai kina fakewa da sana’ar Tuwo-Tuwo da kike yi ki ce wai a harkar kike samun kuɗi har kina siyan gidan naira Miliyan 700 a Abuja. Na san komai kuma kin sani.”
” Kin canja sunan ki saboda karya, sannan auren ki uku. Bayan kin rika zuga ƴaƴan mu su rika bijire wa mazajen auren su da sunan ‘Feminism’, bayan da bakinta ta ce ba za ta sake auren mai mata ba, sai gashi yanzu ta aure mai mata biyu ma.
Sai dai kuma Layla ba ta ce komai ba amma mijinta Honarabul Gagdi ya maida wa Marshal martani, in da ya ce sai ta yi aman duka waɗannan hotuna da ta ke ikirarin ta na da su.
” Na ta wa sa ne,ba a taɓa mini Layla in yi shiru, sai ta yi aman waɗannan hotuna da ta ce ta na da su. Ba a taba min iyali ma in yo shiru.
Discussion about this post