Gwamnatin Tarayya ta cire malamai da ma’aikatan jami’o’i, manyan kwalejojin fasaha da manyan kwalejojin ilmi mai zurfi daga tsarin biyan albashi na ƙeƙe-da-ƙeƙe, wato IPPIS.
Haka nan kuma baya ga albashi, hatta kuɗaɗen alawus-alawus ɗin su zai riƙa tafiya ne kai tsaye asusun bankunan su, ba tare da bin-diddigin ƙwalailaicewa bisa tsarin ‘Integrated Personnel Payment System’, wato IPPIS ba.
Gidan Talbijin na Channels ya ruwaito Ministan Harkokin Ilmi Tahir Mamman ya shaida wa manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa wannan albishir ga malamai da ma’aikatan manyan makarantun gaba da sakandare.
Ya yi bayanin ne Fadar Shugaban Ƙasa, bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa a yau Laraba.
Mamman dai ya yi bayanin a lokacin da sauran ministoci ke tare da shi a wurin taron.
Ya ce wannan umarni na cire IPPIS a biyan albashi da alawus na malamai da ma’aikatan jami’o’i da manyan makarantun gaba da sakandare, ya fara aiki nan take.
Ya ce daga yanzu shugabannin jami’o’i ba su buƙatar karakainar yawan zuwa Abuja domin bin ba’asin albashin ma’aikatan su.
Tun farkon shigo da tsarin IPPIS cikin 2020 dai karatu ya durƙushe, saboda ƙungiyoyi musamman na ASUU da sauran su, sun ƙi amincewa da tsarin.
Discussion about this post