Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda Ya sanya adalci ya zamanto ginshikin da ya tsayar da sama da kasa. Ina shaidawa lallai babu abun bautawa da gaskiya sai Allah; kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad (SAW) bawan Allah ne kuma Manzonsa ne.
Allah yayi dadin tsira da aminci a bisa shugabanmu Annabi Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa da matansa da duk wadanda suka yi imani da shi kuma suka yi ayukka na kwarai har zuwa ranar tashin Al-kiyamah, ranar sakamako.
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Ku sani, lallai Allah Subhanahu wa Ta’ala Ya umarce mu da tsayar da adalci a bayan kasa, kuma ya tabbatar da cewa da adalci ne sama da kasa suka tsayu, kuma sanadiyyarsa ne zaman lafiya yake wanzuwa.
Kuma magabatan mu na kwarai sun fadi wata ka’idah da take cewa:
“Allah yana taimakon daular da ta tsayar da adalci koda daula kafira ce; a yayin da Allah Yake durkusar da daular da take zalunci koda Musulmi ne yake shugabancinta.”
Sannan Allah Madaukakin Sarki Ya umarci bayinsa da su tsayar da adalci tsakaninsu ta kowane hali, domin samun zaman lafiya mai dorewa, a inda Yace:
“Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayin daka domin Allah, masu shaida da adalci. Kuma kada kiyayya da wadansu mutane ta dauke ku a kan ba za ku yi masu adalci ba. Ku yi adalci shine mafi kusa da takawa (tsoron Allah).”
Kuma Allah Ta’ala Yace:
“Kuma idan kun fadi magana to ku yi adalci, kuma koda ya kasance a kan ma’abuci zumunta ne….”
Kuma Allah Ta’ala Ya sake cewa:
“Lallai Allah Yana umurninku da adalci da kuma kayutatawa…”
Ya ku bayin Allah! Yanzu sai mu tambayi kawunan mu tsakani da Allah, shin yanzu akwai adalci a tsakankanin mu kuwa?
Adalci dai shine sanya komai a inda ya dace, a lokacin da ya dace. Adalci shine tafiyar da kowane abu ta hanyar tsari da mutunci da sanin ya kamata. Kuma adalci shine bai wa kowa hakkinsa, da bai wa duk wani mai hakkin hakkinsa.
Addinin mu na Musulunci, addini ne da yazo domin ya tabbatar da cikakken adalci a bayan kasa. Kuma yazo ya mayar da al’ummar duniya baki daya a kan turbar adalcin da suka yi nesa dashi, wajen ibadarsu da hada-hadarsu da mu’amalolinsu da tsarin mulkinsu da siyasarsu da alakarsu ta kasa-da-kasa, da dai sauransu.
Musulunci yazo da adalci kuma yana karfafarsa a ko’ina aka same shi. Yana lale da marhabin da dukkanin wanda yake dauke da adalcin, kamar yadda a daya gefen kuma yake fada da zalunci da rashin adalci a duk inda aka same shi.
Ku sani, addinin mu na Musulunci bai yarda da zalunci ba, kuma bai yarda da zama karkashin wulakanci da zalunci ba. Addinin Musulunci ya umurci Musulmi da su tashi tsaye wajen yakar zalunci da kawar da shi, da tabbatar da adalci a bayan kasa.
Cikakken adalci da babu wata tawaya a cikinsa yana cikin Musulunci, rashin adalci kuwa, shine yin watsi da Musulunci da abinda yake dauke dashi na adalci da sanin ya kamata.
Adalci wata kima ce da Martaba da akan same su a duk inda mutane masu cikakken hankali suka hadu, ko da kuwa ba Musulmai bane, domin duk masu lafiyayyen hankali sun tabbatar da muhimmancin adalci da wajabcin aiwatar da shi.
Manzon Allah (SAW) ya tura sahabbansa (RA) su yi Hijrah zuwa garin Habasha domin gujewa muzgunawar mushirikan zamaninsa, yace masu:
“Ku tafi garin Habasha domin kuwa akwai wani Sarki a can wanda ba ya bari a zalunci wani a wurinsa.”
Shugaban Habasha, wato Najjashi, a lokacin ba Musulmi bane.
Zamu iya fahimta a nan cewar kenan akan iya samun adalci a wurin wanda ba Musulmi ba. Domin Najjashi (shugaban Habasha) ba Musulmi bane, amma kuma shi abun buga misali ne wurin adalci. Shi yasa ma har Manzon Allah (SAW) ya tura sahabbansa wurinsa.
Kamar yadda zamu iya fahimtar cewa ashe al’ummomi masu bambancin addini da yare da asali su kan iya zama wuri daya, har su iya fahimtar junansu, matukar dai akwai adalci da sanin ya kamata a tsakani.
A yau idan muka duba, za mu ga cewa lallai an jarabce mu da mummunan zalunci da rashin adalci da tauye hakkin juna a tsakaninmu. Mun yi nisa da koyarwar addinanmu, mu ka dauki hanyar zaluntar junan mu, shi yasa muke cikin halin da mu ke ciki a yau!
A yau har ya zama abun kwatance, irin adalcin da kasashen Turai su ke yiwa talakawansu ta dukkanin bangarorin rayuwa, wanda har ya jawo, da yawan mutane su na gwammacewa yin hijirah da tare wa kasashen Turai, domin tsira da rayuwarsu da mutuncinsu. Yayin da namu shugabannin na kasashen afrika, suka zama kuraye da zakuna da beraye da Fir’aunoni.
Rayuwar mutunci da ‘yanci da samun hakkokinmu yadda ya kamata, ba tare da tsangwama da tsana da barazana ga rayukanmu da mutuncinmu ba yayi wahala.
Mu sani, tsayar da adalcinmu da sanin ya kamatanmu shine zai sanya wasun mu suyi sha’awarmu, har suyi sha’awar kasashenmu. Haka nan shine zai jawo hankulan adilan mutane wadanda ba Musulmai ba su kalli addininmu da girmamawa da nazari, har Allah ya jawo wasunsu zuwa ga Musuluncin.
Don Allah ku duba ku gani, adalcin “Najjashi” ya kai shi ga Musulunci kai tsaye, bayan ya ga irin adalcin da sahabbai suke dauke dashi. Kuma adalci shine ya lankwaso da Bilkisu har ta mika wuya ga Annabi Sulaiman, ta amshi Musulunci kai tsaye. Adalci shine ya sanya miliyoyin al’ummomi karbar Musulunci a hannun Firimiyan jihar arewa, wato Sardaunan Sakkwato a arewaci, tsakiya da kudancin Najeriya.
Mutane ba su damu da sunanka ba matukar ka tsayar da adalci, ka tsare rayukansu, da mutuncinsu, da addininsu, da dukiyarsu, da hankulansu!
Tsayar da adalci a cikin rayuwa ginshiki ne babba wurin kawo zaman lafiya, kuma zai taimaka wurin dakile dukkanin wani nau’i na ta’addanci da sace-sacen mutane babu gaira babu dalili.
Al’ummah ba wani abu suke bukata ba a yau, illa shugabanni masu tsayuwa da adalci na hakika; wadanda zasu zamanto abun koyi, masu adalci, da tsari da sanin ya kamata; masu koyi da Annabawa da sahabbai da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Kuma ku sani, adalci dabi’a ce mai kyawo, kuma adalci siffah ce ta girma, kuma dabi’a ce ta masu mutunci. Kalmar adalci, kalma ce mai dadin fada, kuma kalma ce abin soyuwa a cikin zukata, kuma jin ta yana sa sanyi-sanyi da fata na gari a cikin zuciyar duk wanda aka zalunta ko aka yiwa rashin adalci.
Ya ku al’ummah, ku sani, lallai da adalci ne Allah ya tsayar da sama da kasa, kuma adalci shine mai daidaitawa tsakanin al’amurrah, kuma da shine ake samun zaman lafiya a bayan kasa, da shine kuma ake dawowa da kowa hakkinsa. Babu yadda za’ayi a samu adalci tsakanin wasu mutane face sai sun yi rayuwa mai kyawo, kuma mai dadi da natsuwa, da kwanciyar hankali. Sannan kuma su samu tsaro da ci gaba. Sannan babu yadda za’ayi a rasa adalci tsakanin wasu mutane face sunyi mummunar rayuwa maras tsari da kan gado, rayuwa irin ta dabbobi, rayuwar tashin hankali, rayuwar rashin tsaro, rayuwar yunwa, talauci da zubar da jini.
Amma kuma idan shugabanni suka ki ji, suka ki yin koyi da irin wannan adalci na Manzon Allah (SAW), suka ci gaba da yin kunnen uwar shegu da shawarwari da ake ba su, da nasihohi da ake yi masu. Suka ki tsayar da adalci a cikin al’ummah, to wallahi ina mai tabbatar maku da cewa, Allah ya sawwake, babu wanda ya isa ya tsayar da abubuwan da suke faruwa na hayaniya da rashin tsaro da ta’addanci da sace-sacen mutane a yau, a arewa da ma Najeriya baki daya.
Domin duk wadannan abubuwa da suke faruwa na rashin tsaro, ina mai tabbatar maku da cewa wallahi duk abun da ya jawo su shine rashin adalcin da yayi katutu a cikin rayuwar mu! Dimbin matasan arewa an bar su babu mafita babu alkibla, ba-su-ga tsuntsu-ba-su-ga-tarko, basu san in da zasu sa kan su ba; babu abubuwan more rayuwa. ‘Yan uwan mu Fulani an bar su cikin daji, cikin rugage, babu tsari, babu karatun addini ba na zamani, sannan babu abubuwan more rayuwa. Kuma kullun suna jin irin yadda ake yin karya na cewa an kashe makudan kudade domin ci gaban su, amma sam basu-gani-a-kasa! Wannan sai ya haifar da mummunan sharri, domin sai matasan arewa da ‘yan uwan mu Fulani suka shiga kungiyoyin ta’addanci da kungiyoyin barayi. Su ka zama bala’i, suna addabar kasar.
Don girman Allah ka fada man, ta yaya za’a samu zaman lafiya a cikin irin wannan yanayi na zalunci da rashin adalci???
Kuma kullun ‘yan Najeriya, arewa da ‘yan arewa kara talaucewa da tsiyacewa suke yi! Manya sun zama kashin dankali, babba ya danne karami. Kullun sai kokarin kara wa mai karfi karfi ake yi, shi kuwa talaka sai kara talaucewa da tsiyacewa yake yi. Masu hali suna kyamar talakawa, suna gudunsu, sai aka wayi gari da talaka da mai hali ana jin haushin juna. Kuma duk da wannan kuce kuna bukatar a samu zaman lafiya a Najeriya da arewa? Haba dai!
Sannan talakawan Najeriya, bayin Allah, suna kallo, kuma suna jin labarin irin yadda shugabannin mu da ‘yan siyasar mu da masu mulkin mu suke sharholiya da dukiyar kasa. Su kuma an bar su yunwa da talauci da cututtuka da ‘yan ta’adda suna ta halaka su.
Kullun abun da kake ji shine, an saya wa su wane motocin miliyan kaza, an gina wa wane gidan biliyan kaza. An ware wa su wane biliyan kaza na cin abinci da tafiye-tafiyensu. An ware wa su wane biliyan kaza domin duba lafiyarsu. An ware wa matar wane biliyan kaza domin a saya mata motoci. Za’a saya wa wane katafaren jirgi na shakatawa, kai da dai duk wani irin almubazzaranci na rashin hankali da rashin tausayi da rashin imani.
Kuma har kullun in dai har za ka saurari labarai ko zaka karanta ko za ka kalla a kasar nan, to babu abunda za ka ji, daga an kashe wane, sai an sace wane, sai an kai wa kauye kaza ko gari kaza hari, sai an kashe wasu bayin Allah talakawa bisa kuskure.
A wannan kasar tamu Najeriya ce fa, abun bakin ciki, talakawa zasu sha rana, su sha wahala, su kwana a layin jefa kuri’a, su sha yunwa, suyi zabe, su zabi wadanda suke so, amma daga karshe, wasu miyagun ‘yan siyasa, wawaye, jahilai, masu son su rusa kasar nan, masu neman fitina, wadanda basu nufin kasar nan da alkhairi, za su hada kai da wasu miyagun alkalai a kotu, a basu cin hanci, ayi kokarin kwace wa talakawa abun da suka zaba!
Kuma wai duk a cikin irin wannan barna da rashin adalci da yake faruwa a cikin al’ummah, wai suke so a zauna lafiya, haba jama’ah! Wallahi muna yaudarar kawunan mu ne kawai, domin ban ga ta yadda za’a yi a zauna lafiya a cikin wannan yanayi ba.
Ya kamata kowa yaji da kyau, kuma ya sani, wallahi Allah ba zai saukar da zaman lafiya a cikin wannan hali na rashin adalci da rashin tausayi ba.
Kum duk juyin mulki, ko yunkurin juyin mulki da ake yi a kasashen mu na Afrika don Allah me yake jawo shi idan ba zalunci da rashin adalci da rashin imani da rashin tausayin talakawa irin na shugabannin mu ba?
Ai juyin mulki kam yanzu ma aka fara wallahi, in dai har ba’a gyara ba.
Don rashin hankali, da rashin tausayi, da rashin imani, da rashin adalci kun san ya wa wasu kasashe takunkumi, wai domin kare dimokradiyyah. An fada maku cewa, talakawan kasashen nan sun shiga wani irin mummunan hali na yunwa da rashin magani da rashin wutar lantarki, saboda takunkumin nan. Mutane suna ta mutuwa, tattalin arzikin kasashen mu ya shiga halin lahaula, duk da sunan kare dimokradiyyah da kuma yiwa wasu aiki. An roke ku, an lallashe ku, an hada ku da Allah mahaliccin ku, a kan kuyi wa Allah ku tausaya, ku cire takunkumin nan, amma duk kun ki ji, kuma kun ki yiwa Allah.
Alhali ga wata kasa can ta isra’ila tana ta kashe bayin Allah ‘yan Falasdinu, amma duk ba’a sa mata takunkumi domin a kare dimokradiyyah ba, sai ku ‘yan bani-na-iya, yaran turawa. Koda yake bamu sani ba, watakila abunda Isra’ila take yi a Falasdinu, na kisan-kare-dangi, kare dimokradiyyah ne oho!
Ku sani, kamar yadda ake ta fada, shi mulki, yana tabbata ko da da kafirci in dai akwai adalci, amma mulki ba ya tabbata ko da da Musulunci in dai akwai zalunci!
Allah Subhanahu wa Ta’ala ya azurta kasar mu Najeriya da nau’ukan dimbin arziki daban-daban domin amfanin dukkanin mu, arzikin da, wallahi da za’ayi amfani da shi yadda ya dace, yadda ya kamata, da wallahi duk za mu wadatu in Allah yaso, wannan sai yasa a samu zaman lafiya, cigaba da wadata, amma an wayi gari wannan arziki yana karewa cikin aljihun wasu mutane tsiraru! Mutum daya sai ya mallake abunda miliyoyin mutane zasu amfana da shi. Yayi ta shan daularsa, shi da iyalansa, sauran jama’ah suna kallo, wahala tana neman halaka su, kuma a haka wai zaman lafiya muke so!
An wayi gari tsakaninmu ma da Allah mahaliccinmu babu kyau. Allah yace muyi, muki yi, yace mu bari, muki bari. Duk wani abu da kasan Allah baya so, kuma ya hana, na zunubi da sabo, yau an wayi gari a cikin mu akwai masu aikata shi. Kuma wai duk a haka muce muna bukatar zaman lafiya, da samun tsaro! Haba wa, ai Allah ba abokin wasar mu ba ne wallahi!
Ya kamata mu san cewa Allah shine yake samar da zaman lafiya da tsaro da arziki da wadata, amma idan akwai adalci. Idan kuma babu adalci sai Allah ya tayar da wasu tsirarun mutane daga cikin ku su addabe ku da bala’i iri-iri har sai kun gyara kura-kuren ku.
Har kullun, Shugabannin Najeriya sun ki su yarda cewa talakawa suna cikin yunwa da talauci da wahala a kasar nan. Shugabannin Najeriya sun ki su yarda cewa mulkin su bai haifar da komai ba sai wahala da rashin kwanciyar hankali da rashin tsaro. Kullun sai karya ake yiwa mutane cewa komai daidai yake a Najeriya, alhali na rantse da Allah karya suke yi. Ko mahaukaci a yau yasan da cewa ana cikin matsala a Najeriya. Yunwa ta kashe mutane, ‘yan ta’adda su kashe mutane, barayi su kashe mutane.
Tsadar rayuwa, wahala, talauci da yunwa a Najeriya yayi tsananin da ba’a taba fuskantar irinsa ba.
Farashin komai kullun sai kara yin sama yake yi, sannan kuma talaka ba ya da kudin saye. Darajar kudin mu sai kara tabarbarewa suke yi.
Masu mulki suna ta sharholiya, su da iyalansu da dukiyar al’ummah. Shi yasa aka wayi gari a yau, tsakanina da Allah, talakan Najeriya baya jin dadin wannan mulkin na Shugaba Bola Ahmad Tinubu!
Ina kira ga shugabannin Najeriya da su sani, wallahi talakawa fa suna cikin wahala a kasar nan! Kuma wannan ba komai ya jawo shi ba illa rashin adalci, hakan sai ya haifar da mummunan rashin tsaro, kamar yadda muke gani a yau!
Sannan ina kira da ku kiyaye, ku guji fushin talaka, kar ku yarda ku kure talakawa, kar ku bari hakurin su ya kare, kar ku yarda ku kai su bango. Domin idan tura-ta-kai-bango, talakawa suka bijire, to sai yadda hali yayi.
To ai ko yanzu duk wani mutum mai hankali ya san da cewa ran talakan Najeriya a bace yake kwarai da gaske. Hakurin da ake ta basu ne, ana ta lallashinsu, da kuma addini da yake taka masu burki, shine yake tasiri, yake hana talaka yunkurawa. Amma kar ku yarda ku kure wannan hakuri na talakan Najeriya.
Nayi imani da Allah cewa, da za’a taimaka, da taimakon Allah, a rage wannan radadin wahala da ke damun mutane, kuma a samar wa da dimbin matasanmu da abun yi, a rage zaman banza da rashin aikin yi, a kula da ‘yan uwan mu Fulani da ke cikin dazuzzuka da rugage yadda ya kamata, a sasanta tare da yin sulhun gaskiya tsakanin mutane da kabilu daban-daban, a yafi juna, ayi kokarin tsayar da adalci, to da za’a samu saukin rashin tsaron nan da sace-sacen mutanen nan da ke damun mu, In Shaa Allahu!
Daga karshe, ina addua da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya kawo muna mafita, ya kubutar da mu daga wannan mummunan hali da muke ciki. Ina rokon Allah ya ganar da shugabannin kasar mu ta Najeriya, su fahimci halin da ake ciki, kuma ya basu ikon gyarawa, amin.
Allah Yayi dadin tsira da aminci ga shugabanmu Annabi Muhammad (SAW), da alayensa, da sahabbansa, da wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Wassalamu Alaikum,
Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samunsa a lambar waya kamar haka: 08038289761.
Discussion about this post