A ci gaba da fallasa gagarimar satar da ake zargin Godwin Emefiele ya ɗirka a CBN, Mai Bincike na Musamman, Mista Obazee na zargin sa da yi wa Naira tiriliyan 26.627 kulli-kirciya, ta yadda ya nunke ‘yan Najeriya da gwamnati baibai.
An kuma zarge shi da ajiye maƙudan kuɗaɗen korona, wato COVID-19 a inda ba can ya kamata a ɓoye su ba.
Kada dai a manta CBN ta bai gwamnatin tarayya bashin Naira tiriliyan 27 a zamanin gwamnatin Buhari, ba tare da sanin Majalisar Dattawa ba.
PREMIUM TIMES ta buga labarin ‘Yadda Sabiu Tunde ya ba Emefiele shawarar a sauya wa Naira launi’.
A ci gaba da bankaɗo harƙallar gagarimar sata da gadangarƙamar karkatar da maƙudan biliyoyin kuɗaɗen Najeriya da ake zargin tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya tafka, Mai Binciken Harƙalla na Musamman ya damƙa wa Shugaba Bola Tinubu rahoton abin da ya bankaɗo a CBN, wanda PREMIUM TIMES Hausa ta fara bugawa daki-daki.
Cikin rahoton, Mai Bincike Obazee ya bayyana cewa tun asali CBN ya aika wa Kwamitin Gwamnonin CBN shawarar za a sauya launin kuɗi.
Babban Daraktan Hada-hadar Kuɗaɗe na lokacin, Ahmed Umar wanda ke ƙarƙashin Mista Folashodun ne aka sa ya rubuta masu wasiƙar a ranar 25 ga Agusta, 2022.
Katsam, wata ɗaya bayan wasiƙar, sai Emefiele ya ce wai ya haɗu da tsohon hidimin tsohon Shugaban Muhammadu Buhari, wato Sabiu Tunde a Fadar Shugaban Ƙasa, a ranar 6 ga Oktoba, 2023, wanda ya shaida masa cewa gara ma a sauya launin kuɗi.
“To a wannan ranar Gwamnan CBN ɗin ya rubuta wa Shugaba Buhari shawarar sauya launin kuɗi, kuma a ranar ce ya sa wa takardar hannun amincewa.
“Sai dai kuma Buhari ya bada umarnin a buga kuɗaɗen a cikin gida Najeriya. Sai dai kuma da aka tuntuɓi Kamfanin Buga Kuɗaɗen Najeriya, wato Nigerian Security Printing and Minting Plc, ya ce aikin zai ɗauki lokaci kafin ma a tsana sabon launin tukunna.
“Jin haka sai Emefiele ya kinkimi aikin ya kai shi Birtaniya, ya biya fam fam na Ingila har 205,000 ladar zana fallen hoton launin Naira 200, Naira 500 da Naira 1,000.” Wannan fa ba a kai ga maganar bugawa ba ma tukunna.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga wani ɓangare na binciken, inda Mai Binciken Musamman ya ce ya gano kawai Sauya Launin Naira da Emefiele ya yi, zamba da harƙalla ce kawai.
Mai Binciken CBN na Musamman, Obazee, ya bayyana a cikin rahoton binciken da ya gudanar cewa shirin sauya launin kuɗin da tsohon Gwamnan CBN, Goodwin Emefiele ya bijiro da shi, harƙalla ce kwai da zuma tantagaryar zamba.
Ya ce shirin ba a nemi amincewar Hukumar Gudanarwar CBN ba, kuma ba a nemi amincewa a rubuce daga shugaban lokacin ba, Muhammadu Buhari.
Ya ce hakan kuwa an kauce wa Sashe na 19 (1) na Dokar CBN, ta 2007.
“Kawai wata maƙarƙashiya ce Emefiele ya shirya domin damfarar ‘yan Najeriya, musamman manyan ‘yan siyasa. Kuma Emefiele ne ya shirya wannan zambar, shi da mataimakin sa a wancan lokacin, mai suna Folashodun Shonubi.
“Emefiele da Shinubi sun shirya zambar sauya launin kuɗi don su hana wasu manyan ‘yan siyasa kasa cimma burin su. To amma sai abin ya zama masifa da bala’in ƙuncin rayuwa ga ɗaukacin ‘yan Najeriya.”
Obazee ya ce CBN ya yi sabbin kuɗaɗen na N200, N500 da N1,000, kuma Naira bilyan 61.5 ya kashe wajen buga kuɗaɗen, waɗanda ya biya Naira biliyan 31.8 ga ɗan kwangilar. Kuma Naira biliyan 769,562 kaɗai na sabbin kuɗaɗen aka buga.
“Emefiele ya kwashi Naira 1,727,500,000 wai ya biya kuɗin lauyoyin biyo bayan shigar da CBN ƙara da aka yi ta yi, bayan ya sauya launin kuɗi.” Haka Obasee ya bayyana a cikin rahoton sa.
Discussion about this post