Hedikwatar Tsaron Sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa sojoji sun kashe riƙaƙƙen ɗan fashin nan Kachalla Ali Kawaje da wasu kwamandojin ‘yan bindiga uku.
Sauran kwamandojin sun haɗa da Ɗan Muhammadu, Machika da Haro.
Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya sanar wa manema labarai haka, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar, a Abuja.
Ya ce Machika gogarman ɗan ta’adda ne wanda ya ƙware wajen ɗana bam, kuma ƙanin Dogo Giɗe, shi kuma Haro da Ɗan Muhammadu manyan baraden iya garkuwa da mutane ne da kuma kai hare-hare.
Ya ce Sojojin Ƙasa da Sojojin Sama ne suka kai masu hari ta ƙasa da ta sama lokaci ɗaya, a ranar 11 ga Disamba, inda a wurin aka yi nasarar kashe Kacahlla Ali Kawaje, wani gogarman ‘yan ta’adda, wanda ya yi garkuwa da ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Gusau, a Jihar Zamfara.
Edward ya ci gaba da cewa an kashe Kachalla a cikin Ƙaramar Hukumar Munya, a Jihar Neja, tare da wasu ‘yan ta’adda da dama da ke tare da shi a lokacin.
Edward Buba ya ce a farmakin dai an kashe kwamandojin ‘yan ta’adda 38, an kuma damƙe wasu 159 a hannu.
Discussion about this post