Tun ba a kammala ƙidaya sauran ƙananan hukumomi uku ba, ɗan takarar APC ya samu ƙuri’u 402,598, yayin da Dino Melaye na PDP ya samu 37,391, kuma shi ne na uku.
Murtala Ajaka na SDP ya cizga ƙuri’u 187,680.
Ododo wanda ya ke gaba a ƙidayar ƙananan hukumomi 18, ya yi wa Ajaka ratar ƙuri’u 214,918.
Rashin taɓukawar da Dino Melaye ya yi a wannan zaɓe ta ƙara bayyana disashewar tasirin PDP a 2023, a Jihar Kogi.
Discussion about this post