Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, ta bi umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara, ta damƙa wa Ministan Ƙwadago, Simon Lalong satifiket na shaidar lashe zaɓen Sanatan Filato ta Kudu.
Cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na tsohon Gwamna Lalong, Makut Macham ya fitar a ranar Alhamis, ya ce ministan ya karɓi shaidar a ranar Alhamis, a Hedikwatar INEC.
Makut ya ce Kwanishinan Zaɓe na Tarayya, Mohammed Haruna ne ya damƙa masa satifiket ɗin, a Abuja.
Hakan kuwa ya na nuni da cewa Lalong zai iya sauka daga muƙamin Minista ya tafi Majalisar Tarayya kenan.
Lalong zai maye gurbin Napoleon Bali na PDP, wanda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tsige a ranar 7 ga Nuwamba.
Lalong wanda ɗan APC ne, shi ne gwamnan da ya sauka a 2023, bayan ya yi zangon shekaru takwas ya na mulkin Jihar Filato.
Lalong ya taɓa yin Kakakin Majalisar Jihar Filato.
Kuma shi ne Babban Daraktan Kamfen na Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Bola Tinubu a zaɓen 2023.
A zaman yanzu ma Kotun Ɗaukaka ƙara ta cire Gwamnan Filato, Mutwang na jam’iyyar PDP, ta ce ɗan takarar APC ne ya lashe zaɓen. Saura jiran hukuncin Kotun Ƙoli kaɗai ya rage a yanzu.
Discussion about this post