Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gargaɗi dukkan ministocin sa su zage damtse su yi aiki, domin tabbatar da nasarar alƙawurran da gwamnatin sa ta ɗauka da kuma nauyin da aka ɗora wa kowane Minista a ma’aikatar sa.
Tinubu ya bayyana haka a ranar Laraba, inda ya ce ba zai ɓata lokaci ba wajen gaggauta duk wani malalaci ko talasurun minista, tare da cewa shi babu wasu ‘ya’yan bora ko ‘ya’yan mowa a wurin sa.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka a wurin Taron Sanin Makamar Aiki da aka shirya wa Ministoci, Hadiman Shugaban, Manyan Sakatarorin Gwamnatin Tarayya da sauran jiga-jigan Gwamnatin Tarayya.
Taron na kwana uku, an shirya shi ne domin zaburar da su ga aiki tuƙuru, tare da hawa ɗoɗar kan turbar tabbatar da nasarorin Ajandar Farfaɗo da Najeriya, wato ‘Renewed Hope Agenda’.
Tinubu ya tunatar da ministocin ayyuka da nauyin da ya rataya a kan su na yi wa al’umma aiki, waɗanda su ka damƙa masa amanar Najeriya ta hanyar zaɓen sa.
Ya ƙara jaddada ƙudirin gwamnatin sa na tabbatar da tsamo mutum miliyan 50 daga ƙangin talauci, ya na mai cewa, “fatara da talauci ba abin kunya ba ne, amma kuma ba zai yiwu a ce muna fama da talauci ba. Tilas mu tashi mu fatattaki talauci ya fice a guje.”
Ya gargaɗi ministoci kowa ta tashi ya taka muhimmiyar rawar kawo ci gaba a ƙasar nan, a ma’aikatar sa. Sannan ya ce gwamnatin sa ta sa himma sai ta maida yawan al’ummar ƙasar nan ya zama babban jari, ba taron yuyuyu ba.
“A ƙarshen wannan taro, kowanen ku zai sa hannun Yarjejeniyar Amincewa da Fahimta tsakanin ku ministoci, manyan sakatarorin gwamnatin tarayya da ni kai na.
“Duk ministan da ke aiki haiƙar, to ba abin da zai ji tsoro. Idan kuma muka ɗora ka kan sikeli ka kasa yin nauyi, to kora ka gida zan yi. Ba ni da ɗan mowa ko ɗan bora a cikin su. Duk abin da ku ka aikata laifi na za a gani, idan ba abin alheri ba ne,” inji Tinubu.
“Zan ba ku ‘yancin ku, ba zan yi wa kowa katsalandan ba. Na naɗa mace mai jini a jika, Hadiza Bala matsayin mai bin-diddigin ayyukan ku. Wanda duk ke da wani ƙorafi a kan ta, to ya tuntuɓe ni. Wanda ya ga zai iya aiki da ita, to ga ku ga ta nan.”
Discussion about this post