A cikin watanni shida manyan bankunan Najeriya 5 sun samu toliyar Naira tiriliyan 2.3, daidai lokacin da talakawa su ka jin jiki saboda ci gaba da ɗanɗana kuɗar gatarin raɗaɗin tsadar rayuwa
Tattalin arzikin Najeriya, ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziki a nahiyar Afirka ya cukurkuɗe da matsanciyar tsadar rayuwar da ke hauwawa, a kowace shekara, tsawon shekaru 18 a jere kenan.
A wannan shekarar, tattalin arzikin ya shiga dawurwura lokacin da darajar Naira idan aka ɗora ta kan sikelin Dalar Amurka, ta yi zubewar da ba ta taɓa yi a tarihi ba.
To, yanzu kuma saɓat-ta-juyat-tar hada-hada da kuma dungulmin da aka yi wa hannayen Naira na hagu da dama, ya sa yanzu bankuna babu ruwan su, sai badali suke yi da maƙudan kuɗaɗe a sauƙaƙe.
Tun cikin watan Mayu, 2022 Babban Bankin Najeriya, CBN ya ƙara kuɗin ruwa, har sun kai kashi 7.25, lamarin da ya sa bankuna ba su jin jiki tun a cikin watanni shida na farkon Mayu, 2022.
Yayin da bankuna suka yi amfani da tsarin CBN su na ƙara wa masu karɓar lamuni kuɗin ruwa, su kuma su na ƙara samun riba, sai kuma ya kasance karya darajar naira da kashi 40 bisa 100 da Najeriya ta yi, abin ya zame wa bankuna alheri.
Karya darajar Naira a cikin 2023 daga N472.8 zuwa N760.3, a cikin makonni uku na ƙarshen watan Yuni, sai bankunan da suka bayar da ramcen kuɗaɗen ƙasashen waje su ka samu ƙarin maƙudan kuɗaɗe kenan idan su ka canja dalolin da aka maido masu na ramce zuwa naira.
Bankuna 5 manya na Najeriya, FUGAZ, wato First Bank, UBA, Guaranty Trust Bank, Access Bank da Zenith Bank, sun samu jimillar Naira tiriliyan 1.3 a ɓagas a hada-hadar su ta Najeriya, kamar yadda rahoton su na Watanni Shidan Farko na 2022 ya bayyana.
Wannan adadi ya nunka abin da su ka samu a watanni shidan farko na 2021 har sau 17. Domin a watanni shidan farko na 2021 Naira biliyan 74.1 kaɗai suka samu a wannan hada-hadar.
To kuma waɗannan bankuna sun ƙara samun toliyar naira tiriliyan 1 rassan su na ƙasashen waje, adadin da idan aka haɗa da Naira tiriliyan 1.3 da suka samu a Najeriya, sun samu Dalar Amurka daidai da Naira tiriliyan 2.3 kenan idan aka canja su.
Wannan fa ba a ma lissafa abin da sauran bankunan su ka samu ba, da sauran cibiyoyin hada-hadar bada lamuni da ba a lissafa da su ba.
Sai dai kuma wannan tsarin ya bai wa bankuna samun damar rage asara, ko maida maƙudan kuɗaɗen da suke bayarwa ramce ana kasa biyan su.
Discussion about this post