Kotun Majistare da ke Dutse a Jihar Jigawa ta tsare jigon jam’iyyar APC a kurkuku, bisa zargin ɗirka wa ‘yar wanke-wanken gidan sa cikin shege.
An tsare Saleh Idris mai shekaru 56 a kurkuku, wanda shi ne Shugaban APC na Ƙaramar Hukumar Roni, a Jihar Jigawa.
Jami’an tsaron NSCDC ne su ka yi cacikui da shi, a ranar 4 ga Oktoba, bayan yayan yarinyar ‘yar shekara 14 ta kai rahoton sa a ofishin su.
Haka dai Kakakin Labaran NSCDC na Jihar Jigawa ya bayyana a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.
Ya ce daga nan ne hukumar tsaron ta NSCDC ta maka shi a Kotun Majistare da ke Dutse, kamar yadda kakakin mai suna Adamu Shehu ya bayyana.
Shehu ya ce an je an yi gwaji a ɗakin gwaji na asibiti Cibiyar Binciken Laifukan Fyaɗe ((SARC), inda aka tabbatar da cewa, yarinyar “ta na ɗauke da ciki ɗan wata huɗu da sati biyu, kuma jinjirin da ta ke ɗauke lafiyar sa ƙalau.
“Wanda ake zargin an caje shi a kotu, yayin da ake ci gaba da bincike.” Haka dai hukumar NSCDC ta tabbatar.
Mai gabatar da ƙara ya ce Idris ya tafka laifin da ya keta Sashe na 3 na Dokar Afka Wa Ƙananan Yara ta Jihar Jigawa, wadda tilas akwai tanadin hukunci a kan sa.
Majistare Salisu Shehu ya bada umarnin a tsare shi kurkuku, har sai ranar 22 ga Nuwamba, domin a bai wa NSCDC damar kammala cikakken bincike.
‘Yadda Shugaban APC Ya Ɗirka Wa ‘Yar Wanke-wanken Gidan sa Cikin Shege’ – NSCDC:
“Yarinyar mai shekaru 14 ta shaida wa jami’an NSCDC cewa wanda ake zargin ya fara kusantar ta, a wata rana da matar sa ba ta gidan. Bayan ta sha lemun, sai hankalin ta ya gushe, shi kuma ya afka mata.” Haka rahoton NSCDC ya nuna.
Bayan ta dawo cikin hayyacin ta, ya yi mata barazana cewa idan ta kuskura ta sanar wa kowa, to za ta rasa kuɗaɗen ladar aikin ta na wata-wata da ya ke biyan ta.”
Bayanin ya ci gaba da cewa ya bar ta a gidan sa ta ci gaba da aikatau tsawon watanni bakwai ba tare da biyan ta alawus-alawus ɗin ta ba.
“Daga nan ya ci gaba da yin lalata da ita, ba tare ita ɗin ma ta sanar wa kowa ba, har dai ya kai ga ɗirka mata cikin shege.”
NSCDC ta ce an kai rahoton matsalar ga jami’an ta na Roni, bayan wanda ake zargin ya karya alƙawarin zai ɗauki ɗawainiyar cikin da ya yi wa yarinyar.”
Bayan Kungiyar Kare Haƙƙin Jama’a ta Jihar Jigawa ta shiga maganar, domin tausaya wa yarinyar, sai aka maida rigimar a Hedikwatar NSCDC da ke Dutse, a ranar 11 ga Oktoba.”
“Amma wanda ake zargin ya musanta, ya ce bai aikata ba, a lokacin da NSDC ke masa tambayoyi.
Idris ya ce abin da kawai ya sani da yarinyar shi ne ta na aikin ɗauko ruwa gidan sa, kuma sai ranar da ake wahalar ruwa, ba kullum ba.
Sannan kuma ya ce bai taɓa yin lalata da ita ba, kuma bai riƙe mata kuɗi ba.
Tuni dai jam’iyyar APC Reshen Jihar Jigawa sun dakatar da shi, dangane da zargin da ake yi masa. Haka dai Shugaban APC na Jihar Jigawa, ya bayyana a cikin wata wasiƙar da ya aika wa wanda ake zargin.
Ya ce binciken da APC ta yi ya tabbatar masu cewa idan babu ƙura, to ba abin da zai ci gawayi.
Discussion about this post