Wani mai makaranta dake zaman kanta a jihar Delta ya yi wa ‘yar shekara hudu fyade a makarantar sa.
Makarantar ‘Great Leaders International’ makaranta ne dake daukan yara kanana na raino sannan akwai fannin makarantar firamare da fannin sakandare duk a makarantar.
Mai makarantar Kuma Shugaban fannin sakandare Innocent Onwuegbule ya yi wa yarinyar fyade a wani bandaki dake makarantar inda a nan ya yi wa yarinyar allurar, ya yi amfani da almakashi ya farke gaban yarin sannan ya danne ta.
Wani mai Rajin Kare hakkin dan Adam a jihar Harrison Gwamnishu ya sanar da haka a shafinsa dake Facebook ranar Laraba.
Gwamnishu ya ce zuwa yanzu Onwuegbule na tsare a ofishin ‘yan sanda dake Agbor.
A wani bidiyon da ya saka a shafinsa na Facebook Gwamnishu ya ce yarinyar ta dawo gida tana fitsarin jini a gida sannan da mahaifiyar ta duba ‘yarta ne ta gano ta’asar da aka aikata wa ‘yarta.
Ya ce Onwuegbule ya aikata haka ranar 4 ga Oktoba a kauyen Agbor dake karamar hukumar Ika ta Kudu.
A bidiyon mahaifiyar yarinyar ta ce mutane na kokarin tilasta ta wai a bata kudi ta tsuke bakinta amma ita dai ta ce tana son adalci.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bright Edafe ya ce Onwuegbule ya aikata wannan ta’asa ne makonnin biyu da suka gabata kuma rundunar ‘yan sanda na gudanar da bincike akai har yanzu.
Edafe ya yi kira ga mutane da su guji karbar kudin daga hannun muggan mutane irin haka cewa yin haka na daga cikin matsalolin dake hana su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Discussion about this post