Najeriya na sa ran ambaliyar Dala biliyan 10 na kuɗaɗen canji nan ba da daɗewa ba, a cikin makonnin nan.
Ministan Harkokin Kuɗaɗe, kuma Kodinatan Harkokin Kuɗaɗe, Wale Edun ya bayyana haka.
Edun ya yi wannan albishir ne a lokacin da ya ke jawabi wurin taron Majalisar Ƙolin Masana Tattalin Arziki (NES), ranar Litinin, a Abuja.
Watanni huɗu kenan darajar Naira na ci gaba da taɓarɓarewa a kullum, har ta kai ga taguwar darajar ya kai da kashi 50 bisa 100 idan aka auna da gejin Dala da sauran manyan kuɗaɗen ƙasashen waje.
Tun cikin watan Yuni Babban Bankin Najeriya ya bada sanarwar haɗe kasuwar hada-hadar kuɗaɗen waye biyu a wuri ɗaya, lamarin da a kullum ya riƙa karye darajar Naira.
CBN ta ce an yi haka ne don a samu ambaliyar kuɗaɗen waje a cikin Najeriya, daga zuba jari.
Da ya ke jawabi a ranar Litinin, Edun ya ce gwamnati na sa ran ambaliyar biliyoyin daloli cikin makonni kaɗan masu zuwa, ba nan da watanni ba.
Idan ba a manta ba, shi ma Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu a taron na NES, ya ce “za mu iya gina ƙasaitattun birane 6 masu girman Legas, ɗaya a kowace shiyya nan da shekara 10.”
A wurin taron, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa shirin gina ƙasaitattun birane 6 a ƙasar nan, zai iya tabbata a cikin shekaru 10, ba kamar nan da shekaru 60 da ake hasashe ba.
Tinubu ya yi wannan bugun ƙirji ne a lokacin da ya ke jawabi a taron Majalisar Ƙolin Tattalin Arziki (NES), ranar Litinin, a Abuja.
Ya ce idan aka yi aiki kafaɗa da kafaɗa da masu zuba jari, Shirin Samar da Dala Tiriliyan Uku don Gina Ayyukan Raya Ƙasa zai iya tabbata cikin shekaru 10, ba sai nan da shekaru 300 ba.
Shugaba Tinubu ya kwantar wa manyan masu hada-hadar zuba jari hankali, ya na mai cewa ana nan ana gagarimin shirin ƙara bunƙasawa da sauƙaƙa samun kuɗaɗen waje, ta hanyar fantsamowar masu zuba jari a Najeriya.
Sai dai kuma ya ce Najeriya za ta yi maraba da kuma amincewa da duk wata hada-hadar da ta kasance ba ta karya dokokin ƙasar nan ba.
Ya jaddada cewa za a iya gagarimin aikin gina Najeriya tare da haɗa kowane yanki da titinan jiragen ƙasa, bututun gas da nagartattun titinan motoci zai iya tabbata ƙasa da shekaru 20, a kowace shiyya cikin shiyyoyin ƙasar nan shida, kafin 2030.
“Wannan gwamnati za ta yi amanna ne kaɗai da halastacciyar kwangila, musamman idan ana maganar kuɗaɗen waje.
“Duk kwangilolin da gwamnati ta riga ta rattaba wa hannu matsawar halastacciya ce, za a tabbatar an aiwatar da ita bisa yarjejeniyar da aka cimma.
“Gwamnati na ta na ganin irin ƙalubalen da tsarin hada-hadar kuɗaɗe ke fuskanta. Zan iya kwantar maku da hankali cewa gwamnatin mu na bisa ga ƙoƙarin samun kuɗaɗen wajen da ake buƙata, domin dawo da martabar kasuwar hada-hadar kuɗaɗen waje,” cewar Shugaba Tinubu.
Daga nan ya lissafa ajandoji 8 da ya ce gwamnatin sa za ta fi maida hankali a kai, waɗanda ya ce sun haɗa da: Kawar da fatara da talauci, wadata abinci, bunƙasa tattalin arziki, samar da aiki, bunƙasa jarin masu ƙaramin ƙarfi, na matsakaita da manya, jawo kowa a jika, inganta tsaro, bin tsarin doka da oda sau da ƙafa da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa.
Discussion about this post