Babban jami’in majalisar dinkin duniya a Najeriya, Matthias Schmale, ya bayyana cewa kudirin ceton al’umma a duniya na fuskantar kalubale sakamakon rikice – rikice.
Schmale ya bayyana hakan ne a cikin sakon bikin ranar majalisar dinkin duniya na shekarar 2023.
A sakon da ofishin majalisar dinkin duniya da ke Abuja ya rabawa manema labarai, Schmale ya ce rikice – rikicen da ake fama da su a kashashen duniya kamar Ukraine, Falasdinu, Isra’ila, Sudan da Myanmar, da kuma korar shugaban Nijar da akai, na kawo cikas ga kudirin ceton al’umma.
Ana gudanar da bikin ranar majalisar dinkin duniya ne a ranar 24 ga watan Oktoba na kowace shekara kuma an fara gudunar da shi ne a 1945. A wannan shekarar taken ranar shi ne “Hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya tare da Nijeriya don Cimma Tsarin SDGs”
Schmale yayi bayani a kan ka’idoji da ayyukan Majalisar Dinkin Duniya da kuma kalubalen da duniya ke fuskanta a yau.
“A shekarar 2023, ya bayyana cewa, wannan kudiri na fuskantar kalubalen da ba a taba ganin irinsa ba, inda tashe-tashen hankula suka shafi miliyoyin mutane a wurare kamar
“Babban Jami’in ya bukaci kasashen kungiyar su sake jaddada sadaukarwarsu da girmama Yarjejeniyar ta Majalisar Dinkin Duniya, da kuma sabunta kokarinsu na inganta zaman lafiya, yana mai bayyana cewa, wannan shi ne muhimmin sakon Babban Sakataren MDD Antonio Guterres a bana,” Schmale ya bayyana a sakon da aka aikewa al’umma.
A cikin jawabin na sa, Mista Schmale ya yabawa ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya, tare da bayyana alhini kan ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya guda 23 da suka rasa rayukansu a harin ta’addancin da aka kai a ofishin MDD da ke Abuja a shekarar 2011 da kuma abokan aikinsu da ke ci gaba da sadaukarwa a yanayi na tashe-tashen hankula.
“Ya yi alkawarin mayar da hankali wajen magance matsalolin da suka shafi yara da ba su zuwa makaranta, rashin abinci mai gina jiki, cin zarafin mata da ‘yan mata, da bukatun al’umma masu rauni da suka hada da tsofaffi, nakasassu, da ‘yan gudun hijira.
“Har ila yau, ya yi kira ga shugabannin gwamnati da su hanzarta aiwatar da ajandar 2030 sannan ya yi magana game da dimbin damar da Nijeriya ke da ita ta bunkasa da ciyar da kanta gaba, yana mai jaddada bukatar mayar da hankali wajen aiwatar da lamarin bilhakki,” Mista Schmale ya ce.
Babban Jami’in ya jaddada kokarin da majalisar ke yi na kara samun kayan aiki don magance matsalolin kiwon lafiya kamar cuta mai karya garkuwar jiki (AIDS), da tarin fuka, da zazzabin cizon sauro, da kuma tallafa wa samar da zaman lafiya, magance rikice-rikice, da inganta hanyoyin sa ido ga rundunar ‘yan sandan Nijeriya.
“Bugu da kari, ya amince da ayyukan jin kai a jihohin Borno, Adamawa, da Yobe, inda aka bayar da agajin gaggawa ga marasa galihu miliyan 3.6 a farkon rabin shekarar nan.
“Schmale ya kuma tunatar da kowa da kowa cewa dole ne dukkanin ayyukan ci gaba su kasance daga tushe a cikin mutunta hakkin Dan’adam, bayar da shawarar ‘yancin fadin albarkacin baki, da kuma dakile kalaman batanci da kiyayya,” in ji Schmale.
Discussion about this post