Kamfanin hada-hadar kuɗaɗe na Opay, ya ƙaryata zargin da aka riƙa yaɗawa cewa ya na buɗe wa mutane lambar akawun na Opay don hada-hadar kuɗaɗe, ba da iznin su ko umarnin su ba.
Opay wanda kamfanin hada-hadar kuɗaɗe ne ta tsarin bankin ‘online’, ya bayyana haka a matsayin martani da raddi ga zarge-zarge da koke-koken da aka riƙa watsawa a soshiyal midiya, cewa kamfanin ya na amfani da lambobin wayar mutane ya na buɗe masu akawun, ba tare da sani su ko umarnin su ba.
A ranar Talata ce dai kwastomomi da dama su ka shiga shafukan su na Tiwita su na ƙorafe-ƙorafen cewa sun wayi gari sun ga an buɗe masu asusun akawun na Opay ba tare da iznin su ba.
Wani mai sunan shafin Tiwita na @hackSultan ya rubuta cewa: “Yanzu na buɗe na cika da mamakin ganin wai na mallaki asusun ajiya na Opay, haka dukkan iyali na kowa shi ma ya ga an buɗe masa akawun a Opay, ta hanyar amfani da lambobin wayoyin su.
“Amma kuma babu ko ɗayan mu da ya taɓa buɗe akawun da Opay. Shin ta yaya hakan ya zama halas a dokance da Shari’a ce?”
Shi ma wani mai sun @IHarbaty cewa ya yi: “Ka jaraba wannan abin za ka ga ka dace… Ba ni da asusun ajiya a Opay, amma lamba ta na da lambar akawun da su. Amma na yi ƙoƙarin shiga da lambobin iyaye na, abin bai yiwu ba. Amma na ƙanne na duk ya yi, su ma akwai lambar akawun da lambobin wayoyin su duk na Opay. Shin wannan wane irin siddabaru ne?”
Sai dai kuma kamfanin Opay ya aiko wa PREMIUM TIMES da sanarwa cewa wasu lambobin tun a tsakanin 2019/2020 sun buɗe asusun ajiya da Opay.
Kamfanin ya ce alaben su ba ya taɓa buɗewa sai fa ta hanyar da Babban Bankin Najeriya, CBN ya tsara, wanda tilas sai da lambar sirri ta OPT.
Discussion about this post