Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa fiye da ‘yan Najeriya miliyan 90 ba su iya samun wutar lantarki.
Tinubu ya bayyana haka a ranar Litinin, taron tunawa da Shekaru 10 da Sayar da Hannun Karin Wutar Lantarki ga ‘Yan Kasuwa.
Haka kuma shi ne taro na farko na Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Najeriya (NESI), wanda masu ruwa da tsaki su ka tattauna batun wutar lantarki, a Abuja.
Najeriya ta sha fama da matsalar wutar lantarki fiye da shekaru 30 da suka gabata, kuma har yau ba a fita cikin matsalar ba. Duk kuwa da cewa an narka tiriliyoyin nairori wajen gyara ko inganta samar da wutar lantarki.
An ƙiyasta a duk shekara ana Najeriya na narkar da Dala biliyan 29 wajen wutar lantarki, kamar yadda Bankin Duniya ya tabbatar, a cikin rahoton sa.
Cikin 2013 aka sayar da hannun jarin Gwamnatin Tarayya daga wutar lantarki, daga nan kuma kamfanoni suka karkasa ta tare da sayarwa kan su.
An yi haka ne domin inganta raba wutar lantarki a faɗin ƙasar nan.
Da ya ke magana a ranar Litinin wurin taron, Tinubu wanda Mashawarcin Musamman a Fannin Makamashi, Sodiq Wanka ya wakilta, ya ce “shekaru 10 bayan sayar da harkar wutar lantarki ga ‘yan kasuwa, amma har yau buƙata ba ta biya ba, kuma kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba.
“Babban maƙasudin sayar da hannun jarin wutar lantarki ga kamfanoni shi ne domin inganta wutar lantarki a faɗin ƙasar nan.
“Amma kuma shekaru 10 kenan sai dai har yanzu ba a cimma ƙudirorin da gwamnati ta so ta cimma ba, kuma kwalliya na ta biya kuɗin sabulu ba.”
Ya ce an sayar da hannun jarin wutar lantarki ga ‘yan kasuwa bisa ƙudirin samar da migawat na ƙarfin wuta har 40,000 tsakanin 2013 zuwa 2020.
“Sai dai abin takaici har zuwa yanzu ƙarfin wutar Najeriya baki ɗaya bai wuce migawat 4,000 da ɗan ɗoriya ba.”
Discussion about this post