Ba tun yanzu ba nake kwana na tashi da baƙincikin yadda gidan Rediyon Najeriya na Kaduna FRCN, ta koma kusan in ce kufayi, ko kuma in ce gidan ajiye tarkace da tarihin da basu da amfani ga mutanen Arewa yanzu tunda ba a watsa su, masu tasowa su ji su saurara su sani.
Dalili kuwa shine, an kai ga sai a yi mako guda cur gidan rediyon bata aiki kwatakwata. Da na tambayi wasu ko menene labarin tashar AM wanda shi muka fi sani sai suka ce yanzu a FM ɗin Karama ake watsa wasu daga cikin labarai da shirye shiryen tashar.
Tsakani da Allah, Duk wanda ya taso a Arewa musamman daga 1970 – 2000 ya san daraja da karamar da ke gidan rediyon tarayya na Kaduna. Shi ake saurare, shi ake nishaɗantuwa, kai shine dai gatan Arewa.
Tunda aka zamanin mutane irin su Halilu Getso, suka wuce, sauran shugabannin da suka biyo baya kawai sun dai yi aiki ne amma ba su shuka komai ba.
Abun tambaya shine, wai ina shugabannin Arewa wanda suka mori waɗannan kafafe tun suna yara har suka taso suka manyanta, suka amfana da su amma yanzu suka yi watsi da su abubuwan tarihi irin haka.
Yaron da aka haifa shekaru fiye da 10 yanzu bai san irin tasiri da amfani da ma gudunmawar da wannan gidan rediyo ya bada a cigaban Arewa ba.
Yankin kudu sun cigaba matuka a harkar jarida, Arewa sai cika baki, wanda shugabannin yankin masu kishin Arewa suka kakkafa suka bari don mu ƴan baya duk an kashe su ta hanyar rashin iya shugabanci da sata.
Yanzu idan ba FM ba AM ɗin da a baya har a kasashen waje a na ji da saurare ba shi ya mutu murus. Abinda nake kira ga sabon ministan yaɗa labarai, idan akwai wani abu da zai yi ya kafa tarihin da hatta ƴaƴa da jikokin sa za su amfana da su sannan kuma lada da rahama ya lulluɓe shi, shine ya maida hankali wurin ganin an farfaɗo da wannan tasha ta dawo aiki fiye da yadda yake ada.
A dawo da shirye-shiryen da aka sansu a da masu amfani, faɗakarwa da nishaɗantarwa. Sannan kuma da shirye-shirye addini da ake yi domin mutanen Arewa.
Tsakani da Allah, Lalacewar ta yi yawa matsayin da gidan rediyon ke ciki yanzu, wallahi babu ɗaɗi ko kadan musamman idan kasan yadda tashar yake a da.
Lallai minista Mohammed Idris ya kira taron gaggawa game da wannan gidan rediyo a sama masa mafita na dindindin. Amma abin babu ko ɗadin ji.
Allah ya ba da ikon gyara Amin.
Mohd Ibn Mohd daga Abuja, Najeriya.
Discussion about this post