Shugaban hukumar NPHCDA Faisal Shuaib ya bayyana cewa mutum 156 sun kamu da cutar Diphtheria sannan cutar ta yi ajalin mutum 20 tsakanin watanni Maris da Satumba 2023.
Shuaib ya fadi haka ne ranar Laraba da ya kai ziyara asibitin Barau Dikko domin ganin matakan dakile yaduwar cutar da jihar ta dauka.
Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohi bakwai da suke fama da yaduwar cutar a Najeriya.
Ya ce rashin gaggawar kawo mutum asibiti na daga cikin dalilan dake yada cutar sannan kuma ya yi kira da a rika gaggawar zuwa asibiti domin samun magani.
Shuaib ya kuma ce akalla kashi 80% daga cikin wadanda suka kamu da cutar basu yi allurar rigakafi.
“ Muna kira ga gidajen jaridu da su hada hannu da gwamnati domin wayar da kan mutane kan cutar.
Shuaib ya ce rashin yin allurar rigakafi na daga cikin matsalolin da ya sa cutar ke yaduwa.
Shugaban NPHCDA ya yabawa gwamnatin jihar kan kokari wajen yakan cutar sannan ya yi kira ga mutane da su rika yin allurar rigakafi tare da saka takunkumi a duk lokacin da za su asibiti.
Daga nan Shugaban fannin kula da bullar cututtuka na asibitin Barau Dikko Shu’aibu Musa ya ce mutum hudu daga cikin mutum shida din da suka kamu da cutar dake kwance a asibiti sun warke.
Shu’aibu ya yi kira ga mutane da su tsaftace jikinsu da muhallinsu, kare bakonsu a duk lokacin da za su yi tari ko atishawa domin kare kansu da na kusa da su daga kamuwa da cutar.
Discussion about this post