Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya bayyana cewa ya ziyarci shugaban kasa Bola Tinubu ne domin ya yi masa bayani da inda ake da inda aka dosa a jihar Kaduna da irin abubuwan da jihar ke buƙata cikin gaggawa daga gwamnatin Tarayya.
Baya ga haka gwamna Sani ya ce garzaya fadar shugaban kasa ne domin ya gode wa shugaba Tinubu kan goyon baya da yake ba jihar Kaduna a koda yaushe.
” Bayan haka akwai wasu ayyuka da dama da ba za mu iya yin su kai tsaye ba dole sai gwamnatin tarayya ta sa hannu idan muna so mu yi nasara a kansu. Shine yasa muka zo mu tunatar da gwamnati akan haka.
Gwamnan ya ce waɗannan fannoni sun haɗa da fannin tsaro, aikin gona da kiwon lafiya.
” Nan take shugaba Tinubu ya kira wasu ma’aikatun gwamnatin tarayya domin su saurare mu sannan su bamu duk goyon bayan da muke bukata domin samun cigaba.
Discussion about this post