Mambobin Majalisar Tarayya sun goyi bayan a zaɓo majiya ƙarfi daga yankunan mazaɓun da ‘yan bindiga ke ɓarna, a ba su makamai, sannan a horar da su yadda zasu tunkari masu garkuwa da mutane.
An cimma wannan matsaya ce bayan Ɗan Majalisa Kabiru Mai Palace, ɗan PDP daga Zamfara, ya gabatar da wannan koken.
Lokacin da ya ke gabatar da wannan hanzari a madadin sauran ‘yan majalisar tarayya daga Jihar Zamfara, Kabiru ya ce tuni yankin Arewa maso Yamma ya afka a hannun ‘yan bindiga.
“Irin ɓarnar da ‘yan bindiga ke tabkawa har ta isa yankin mazaɓar sa.
Ya ce a Mazaɓar sa kaɗai “an yi garkuwa da mutum 126, cikin su har da ƙananan yara 33, kuma an kashe fiye da mutum 53 duk a cikin wata uku.”
Sai dai kuma Ɗan Majalisa daga Ribas, wato Solomon Bob, ya ce ƙudirin da za a zartas ba shi da wani amfani, domin an sha zartas da irin sa a baya, amma ba a yi komai ba.
Bob ya ƙara da cewa bayan ‘yan Majalisa sun saurari koke-koke daga mazaɓun su, ba su iya yin komai a kan matsalar.
“An daɗe ana magana kan matsalar tsaro, amma ba a yin komai. Don haka babu amfanin kawo wani sabon abu a yanzu, ya kamata a ga an fara da aikata batutuwa ko ƙudirorin matsalar tsaro.
“Mu daina batun ƙudirorin tsaro haka nan, domin shekaru biyar kenan mu na bayyana takaicin da mu ke gani a yankunan da waɗanda suka zaɓe mu su ke, amma ba a yin komai. Kamata ya yi sai mun ga hukumomin da abin ya shafa sun maida hankali kacokan kan matsalar tsaro, sannan za mu ci gaba.”
Sai dai wasu ‘yan Majalisa sun yi masa caa, saboda ba su ji daɗin kalaman da suka fito daga bakin sa ba, har suka riƙa yi masa “ka zauna, ka yi wa mutane shiru.”
Mataimakin Shugaban Majalisa, Ben Kalu wanda shi ne ya jagoranci zaman majalisar, ya ce majalisa na da haƙƙin kare rayukan ‘yan ƙasa.
Ya ce ‘yan Majalisa ba za su iya yin shiru a lokacin da ake fama da matsalar tsaro ba.
A ƙarshe Mai Palace ya roƙi Majalisa ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta hanzarta ceto dukkan waɗanda ke hannun masu garkuwa da mutane. Kuma a yi bincike kan ayyukan ta’addancin da ‘yan bindiga ke aikatawa, tare da hukunta masu hannu.
“Mu na kira ga Babban Kwamandan Askarawan Najeriya ya maida Hedikwatar Tsaro ta koma Arewa maso Gabas, har sai bayan an kakkaɓe ‘yan bindiga an samu zaman lafiya tukunna.
“Kira da a ƙara girke jami’an tsaro a Arewa maso Gabas.”
Wasu ‘yan majalisa nemi a yi irin wannan tsarin a sauran yankunan da ke fama da matsalar tsaro.
Discussion about this post