Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da cewa gogaggen tsohon ɗan jarida, Hamisu Ɗanjibga, ya rasa ran sa ne ta hanyar mumnunan kisan da wani yaro ɗan yayan sa ya yi masa.
Sun ce makashin mai suna Mansur Haruna, ya haɗa kai da wani abokin sa, su ka kashe kawun na sa, saboda kawai ya ƙi amincewa ya zame masa giranto a lokacin da ya nemi shiga aikin soja.
Mansur ya zargi marigayi Ɗanjibga da tare masa hanyar shiga aikin soja, saboda ya ce ba zai iya taimakon sa ba, saboda ba shi da halaye nagari.
‘Yan Sanda sun damƙe Haruna tare da wani abokin sa, wanda ya taya shi yi wa kawun nasa Ɗanjibga mummunan kisa. Sunan abokin Ibrahim Nababa.
Tun da farko dai an nemi inda Ɗanjibga ya shiga, amma an rasa, lamarin da iyalan sa suka shiga damuwa, har suka sanar wa ‘yan sanda.
Daga baya an gano gawar sa a cikin ramin shadda, a bayan gidan sa a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
Ɗanjibga ya yi aiki da Muryar Najeriya, VON tsawon shekaru masu yawa.
A lokacin da suke gabatar wa ‘yan jarida waɗanda ake zargin a ranar Talata, Kwamishinan ‘Yan Sandan Zamfara, Mohammed Dalijan ya ce makasan sun caccaka masa wuƙaƙe a sassa da dama na jikin sa.
‘Yadda Suka Yi Yunƙurin Garkuwa Da Shi, Kafin Su Kashe Shi:
Dalijan ya ce waɗanda ake zargin da kan su suka bayyana wa ‘yan sanda cewa su ne suka kashe shi, amma da farko niyyar sace shi su yi garkuwa da shi suka yi.
Sun ce ganin sun kasa yin nasarar tafiya da shi ne, sai suka kashe shi, ganin ya na neman ya fi ƙarfin su.
Kwamishinan ‘Yan Sanda ya ƙara da cewa Mansur ne ya fara burma wa Ɗanjibga wuƙa har sau uku, shi kuma Nababa ya datsa masa adda har sau biyu bisa kan sa.
“Shi wanda ake zargin, wato Mansur, ɗan yayan Ɗanjibga ne. Ya na zaune ne a gidan mamacin da ya kashe ɗin nan a Gusau. Ya nemi ya shiga aikin soja, amma kawun sa Ɗanjibga ya ce: “A irin munanan ɗabi’un ka, gaskiya ba zan iya tsayawa a matsayin giranto ɗin ka ba.
“Alhaji Ɗanjibga ya kore shi daga gidan sa, sai ya tafi ya zauna wurin abokin sa Ibrahim Nababa. To a gidan abokin ne su ka shirya yadda za su sace Ɗanjibga.
“Bayan gama tsara komai, sun tafi gidan mamacin, suka same shi tare da ƙoƙarin arcewa da shi, amma abin ya faskara.
“Ɗanjibga ya ce masu, ‘Yanzu kai ɗa na irin sakayyar da za ka yi min kenan? To ba zan je ko’ina ba.”
Dajilan ya ce daga nan su ka bi shi da suka da sara, har ya faɗi ya mutu. Su ka ɗauki gawar suka jefa cikin ramin shadda na wata makarantar Islamiyya.”
Ɗanjibga ya shahara sosai wajen rahoton garkuwa da ta’addancin ‘yan bindiga a Zamfara.
Allah ya gafarta masa, amin.
Discussion about this post