Babban jidali da bala’i a wayi gari magidanci mai iyali ya shafe kwana da kwanaki bai ci ba, kuma bai samu ya kai wa iyalin sa sun dafa sun ci, kai ko da ɗanyen ne ma sun ci.
Bala’in da ya zarce wannan muni shi ne idan matsalar babu ɗin ta kai gargarar da har yunwa ɗin ta kai ga yi wa marasa galihu ɗauki-ɗai-ɗai, daga duniya ta na cilla su lahira.
Haka ta faru da wata budurwa mai suna Aisha, wadda babu wanda ya san musabbabin rasuwar ta, har sai bayan an binne a kabari, kafin a tashi sai mahaifin ta ya sanar da masu makoki cewa, “babu abin da ya samu A’isha, tsananin yunwa ce ta kashe ta!” Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un.
Mahaifin A’isha mai suna Malam Garba (mun ɓoye sunan sa na ainihi), ya fito ne daga wani yanki a Jihar Adanawa. Ya shaida cewa yunwa ce ta kashe ‘yar sa ta farko, Aisha. Ya ƙara da cewa raɗaɗin tsadar rayuwa ya afka masa shi da iyalin sa sakamakon daminar bana ba ta yi masa albarka ba.
Ya ce, “iyali masu fuskanci tsananin yunwar da mukan shafe makonni da dama ba a iya ɗora girkin abinci sau biyu ba.
“Da A’isha ta ga matsalar rashin abincin sai ƙaruwa ta ke yi, sai ta ce ‘ai da yunwar banza gara mai dalili’, sai ta fara azumin nafila a kullum, don kawai ƙannen ta su samu su ɗan riƙa haɗawa da na ta kason abincin su na ci.
“Marigayiya A’isha ta sadaukar da abincin ta ga ƙannen ta, don su samu su ɗan riƙa ci kafin mu kwanta barci.
“Wasu lokuta kuma idan A’isha ta samu ta ɗan ci wani abu a lokacin buɗa-baki, ta na sahur da asubahin ma gagarar ta ya ke yi.
“Ranar da ta ɗauki azumi na 30, sai ta fara kyara aman jini a duk lokacin da ta yi tari. Bayan kwanaki sai rai ya yi halin sa.” Inji Malam Garba, mahaifin ta.
Jama’a sun tausaya wa mahaifin A’isha bayan sun ji wannan labari marar daɗin ji, kuma mai dugunzuma zukata. Wasu kuma sun riƙa yin alƙawarin tallafa wa iyalin Malam Garba, tare da taimaka wa ƙannen Aisha domin su tsira daga yunwar da ta nuƙurƙusar da dukkan ‘yan gidan su.
A shekarar 2022 dai an fuskanci gagarimar ambaliya a yankuna da yawa na Arewacin Najeriya, sakamakon ruwan sama mai yawa, kuma mai ƙarfi.
Koguna da ƙoramu da gulabe sun cika maƙil. Madatsun ruwa sun cika, sun batse har sun riƙa ɓallewa, musamman madatsun ruwan Kamaru da suka haddasa ambaliya a jihohi 31 daga 36 na Najeriya.
Cibiyar Bincike ta Majalisar Ɗinkin Duniya, mai suna UNOSAT, ta bayyana cewa tsakanin 13-17 ga Oktoba, 2022 ambaliya ta yi wa sama da mutum miliyan 6.6 babbar barazana. Kuma kusan fiye da murabba’in kilomita 30,000 ne ambaliya ta mamaye.
Jihar Adamawa na cikin jihohin da ambaliyar ta fi yi wa babbar ɓarna, inda aka ƙiyasta ta shafi sama da mutum 260,000 a jihar. Kuma kuma ambaliya ta mamaye kilomita 1,000 a jihar, tare da lalata dukkan amfanin gonar da ke wuraren da ambaliyar ta mamaye.
Hukumar Agajin Gaggawa ta Jiha, ta ce ambaliyar ta afku sanadiyyar ruwa mai ƙarfin da aka riƙa yi daga 11 zuwa ga Yuli, har zuwa 24 ga Oktoba, 2022.
Ambaliyar ruwan da ya riƙa darkakowa daga Kamaru ya haddasa cika da batsewar Kogin Benuwai, wanda hakan ya haddasa ambaliya a Jihar Adanawa.
Sannan kuma ambaliyar ta ƙara muni bayan Kamaru ta ɓallo ruwan Madatsar Ruwa ta Lagdo, inda ruwan ya malalo Arewacin Najeriya, ya lalata amfanin gona da dukiya mai tarin yawa.
Shugaban SEMA na Jihar Adamawa, Suleiman Muhammad, ya ce “Binciken HNO na 2022 ya tabbatar da cewa sama da mutum miliyan 2.45 ne suka rasa muhallin su a Jihar Adamawa, su ka koma tsuguno a sansanonin masu gudun hijira.”
Wakilin mu ya je garin Gerio, ɗaya daga cikin garuruwan da ambaliyar ta fi yi wa mummunar illa.
Wani ɗan jarida mai suna Yakubu Abdullahi, ya shaida wa wakilin mu cewa tsawon sama da shekaru 30 kenan, duk lokacin da Kamaru ta ɓalle ruwan Dam ɗin Lagdo, sai ambaliya ta yi mummunar ɓarna a yankunan Najeriya.
Sai dai wani kuka ya ce ba fa laifin ruwan da Kamaru ke ɓallowa a kowace damina ne kaɗai ke haddasa masu asarar amfanin gona ba. Ya ce su kan yi noman rani da noman damina. Amma a shekarar 2021 sun fuskanci fari da ƙarancin ruwa daga dam ɗin Gerio. Ya ce kashi 80 zuwa kashi 90 bisa 100 na shinkafar da suka noma cikin 2021 duk bushewa ta yi, ba su ci gajiyar ta ba. Saboda Kamaru ba ta sako ruwa a shekarar ba.
“To da muka zuba shinkafa a 2022 mai yawan gaske domin noma har da wadda muka yi asara a 2021, sai ruwa mai ƙarfi ya zame mana bala’i, duk ya yi tafiyar-ruwa da shinkafar a cikin gonakin mu.”
Ya nuna cewa ruwan da ke malalowa daga Kamaru ba bala’i ba ne a wurin su. “Ba za mu yi saurin cewa mun yi nasara ba kam. Amma abin da ke addabar mu shi ne ruwan sama mai ƙarfin gaske, ba ruwan da ke malalowa daga Kamaru ba.”
Discussion about this post