Rundunar ‘Operation Sweep’ da aka kafa a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, ta kama mutane 400 tare da wasu motoci 50 da suka karya doka a Abuja.
Kwamandan rundunar kuma Shugaban ‘yan sanda Umar Kadiri ya sanar da haka ranar Litini da yake ganawa da manema labarai a Abuja yayin da rundunar ke rusa gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba da korar ƴan tireda daka yi a titunan jihar.
Rundunar ta kuma rusa tashar motocin da aka gina ba bisa ka’ida ba, kawar da haramtattun gine-gine a kan tituna da ruguza da kona maɓoyar barayi.
Rundunar ta gudanar da wadannan aiyukka a kasuwar Utako zuwa layin A.E Ekukinam zuwa tashar mota dake Jabi da kewaye daga ranar Juma’a zuwa Litini
Kadiri ya ce wasu daga cikin mutanen da suka kama har an yanke musu hukunci a kotu.
Ya ce rundunar ta yi haka ne domin farfado da tsaftace muhalli da samar da tsaro a Abuja.
Bayan haka shugaban hukumar AEPB Kaka Bello ya ce ministan Abuja Nyesom Wike ya kafa rundunar domin tsaftace Abuja.
Bello a dalilin haka ya yi kira ga masu kangon gini da su yi gaggawar kammala gine-ginen su.
Rundunar sojin kasa, rundunar sojin sama da ruwa, hukumar kiyaye hadurra da AEPB na daga cikin mamnbobin rundunar ‘Operation Sweep FCT’ da aka kafa.
Saura sun hada da wakilan ‘yan sandan Najeriya, wakilan hukumar shige da fice, jami’an tsaron Najeriya na Sibul Difens da jami’an tsaro na SSS.
Discussion about this post