Jami’an ‘yan sandan Enugu sun kama Gabriel Gibson mai shekara 27 da aka samu da laifin yi wa matar abokinsa fyade.
Kakakin rundunar Daniel Ndukwe wanda ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar ranar Laraba ya ce Gibson da aka fi saninsa da suna ‘Ogidi’ ya aikata wannan laifi da misalin karfe biyar na safiyar ranar 18 ga Agusta.
Ndukwe ya ce a wannan rana Ogidi ya ziyarci gidan abokinsa duk da cewa baya nan a gari ya danne matarsa.
Ya ce ‘yan sandan dake aiki a Oji-River ne suka kama Ogidi da misalin karfe 10 na safen ranar 21 ga Agusta Kuma zuwa yanzu ya na tsare a ofishin ‘yan sandan.
Ndukwe bai fadi kauyen da karamar hukumar da wannan abin ya faru ba amma ya tabbatar cewa da zarar jami’an tsaro sun kammala bincike za a maka Ogidi kotu domin yanke masa hukunci.
Discussion about this post