Wani direba mai suna Sa’idu Tanko da ke tuka motar hayan na fasinja a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari ya rasa ransa bayan da ‘yan bindiga suka bude wa motar wuta, ta tsaya sannan suka kwashe fasinjojin motar kaf suka yi awon gaba da su.
Tanko wanda ya dan asalin yankin Tegina ne da ke karamar hukumar Rafi ta Jihar Neja, ya debo fasinjoji daga Tegina ne zuwa Gusau a Jihar Zamfara a ranar Litinin, yayin da ‘yan ta’addan suka kai wa motarsa hari a Manini.
Abokin marigayin, Hassan Ahmad, wanda ya shaida yadda aka fitar da gawar Tanko daga inda aka kai harin a ranar Talata ya ce ‘yan ta’addar sun sace fasinjoji bakwai bayan harin.
Haka kuma ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa marigayi Tanko ya rasu ya bar mata 4 da ‘ya’ya 12.
An samu rahoton cewa ‘yan bindigan sun kira ‘yan uwan daya daga cikin wadanda suka sace kuma sun bukaci a biya naira miliyam 30 kudin fansa, kafin su sake shi.
Shugaban kungiyar masu ci gaban masarautar Birnin-Gwari (BEPU), Ishaq Usman, ya ce kisan direban na daya daga cikin hare-haren da ‘yan ta’adda suka kai kan babbar hanyar Birnin Gwari- Kaduna a ‘yan kwanakin nan.
“A cikin makonni hudu da suka gabata lamarin ya kara ta’azzara, har ya zuwa yau (27 ga Satumba) ‘yan bindiga suna kai hari kan matafiya a kan babbar hanyar, mutum bai isa ya bi hanyar Birnin-Gwari-Kaduna ba tare da rakiyar jami’an tsaro ba,”
Usman ya roki hukumomin Najeriya da su kafa rundunar soji a Katakaki da ke gundumar Kakangi a yammacin Birnin-Gwari sannan a saka sojoji akalla 1,000 da za su rika aiki a wannan yanki.
Discussion about this post