Christopher Danjuma ya koma bakin aikinsa a matsayin Babban Kocin kungiyar Mata ‘yan kasa da shekaru 20, Falconets, bayan wani tsari na tantancewa kwamitin NFF ya yi.
Kwamitin ya gabatar da shawararsa kuma kwamitin zartarwa na NFF ya amince da hakan kamar yadda wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba.
Danjuma, wanda ya dauki nauyin horar da manyan mata na kasa Super Falcons, na wucin gadi sau biyu, ya jagoranci Falconets zuwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya na mata na FIFA ‘yan kasa da shekaru 20 a bara a Costa Rica.
Yahaya Audu wanda shi ne mai horas da masu tsaron ragar kungiyar shi ma ya koma matsayinsa.
Discussion about this post