Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta bayyana cewa jami’an ta sun kama wani Ja’afar Adamu mai shekaru 36 da ya yi wa matar makwabcinsa mai shekara 21 fyade a Anguwan Diocese Kala’a dake karamar hukumar Hong.
Kakakin rundunar Suleiman Nguroje ya sanar da haka ranar Talata a garin Yola.
Nguroje ya ce ‘yan sanda sun kama Adamu ranar 15 ga Satumba
“Jami’an tsaron sun samu labarin cewa a wannan rana bayan Adamu ya tabbatar makwabcinsa bashi gida ya afka gidan sa.
“Adamu ya shiga gidan yana sanye da bakin kyale da ya rufe fuskarsa da shi da wuka wanda da shine ya yi wa matar barazanar zai kasheta idan bata bashi hadin kai ba.
“Sai dai yayin da yake yi mata fyaɗen sai bakin kyalen ya warware, sai ya tashi ya arce.
Kakakin ya ce mijin matar ne ya kawo kara ofishin ‘yan sandan dake Kala’a.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Afolabi Babatola ya ce rundunar za ta kai Adamu kotu da zarar ta kammala bincike.
Babatola ya yi kira ga mata da su rika fitowa suna kawo karar wanda ya ci zarafin su cewa yin haka ne kadai zai iya kawo karshen matsalar a jihar.
Discussion about this post