Shugaban ƙasar Nijar da sojoji suka hamɓare, a karon farko ya yi magana daga inda ya ke a tsare.
Bazoum ya yi magana ranar Juma’a, kwanaki tara bayan hamɓarar da Gwamnatin sa.
Da ya ke magana a inda ya ke tsare, Bazoum ya ce hamɓarar da Gwamnatin sa gangaci ne, kuma babu wani dalili ko hujjar da sojoji za su kifar da gwamnatin sa, wadda al’ummar Nijar su ka zaɓe su.
“Juyin mulkin da sojoji suka yi min a ranar 26 Ga Yuli, ba shi da wani dalili ko hujja.
“Domin juyin mulkin zai haifar da mummunan sakamako a yankin mu da ma duniya baki ɗaya.”
Haka Bazoum ya faɗa a shafin sa na X Tiwita.
Babu wata sanarwa mai tabbatar da cewa bayanan sa ne, amma ganin yadda AU, Bankin Duniya da Bill Gates ke bibiyar shafin na sa, hakan ya ƙara tabbatar da cewa Bazoum ɗin ne ya yi rubutaccen bayanin.
Bazoum ya roƙi a ƙasashen ECOWAS da duniya kada a bari sojoji su gurgunta dimokraɗiyya.
Yayin da Bazoum ya roƙi Amurka da sauran masu faɗa a ji, su taimaka masa mulki ya koma hannun sa.
A cikin jawabin na sa, ya bayyana irin gagarimar nasarorin da gwamnatin sa ta samar wajen tsaron Nijar yankin ECOWAS.
Haka kuma Bszoum ya yi Allah wadai ƙasashen Mali da Burkina Faso, waɗanda suka nuna goyon bayan su ga gwamnatin sojojin Nijar.
A ranar Alhamis ce kuma wata tawagar ECOWAS ta dira Yamai, domin tattaunawa da sojojin mulkim
Tawagar da Ƙungiyar ECOWAS ta tura Jamhuriyar Nijar, ta isa birnin Yamai domin tattaunawa da sojojin mulkin ƙasar, waɗanda suka ƙwace iko daga hannun shugaban farar hula, Mohammed Bazoum.
Tawagar wadda ke ƙarƙashin tsohon Shugaban Mulkin Soja na Najeriya, Abdulsalam Abubakar, ta bar Abuja ta bar Abuja zuwa Yamai a ranar Alhamis, bayan ta gana da Shugaba Bola Tinubu.
Tawagar dai ta mutum uku ce, kamar yadda Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale ya fitar da sanarwa.
“Shugaban ECOWAS Bola Tinubu ne ya tura tawagar zuwa Jamhuriyar Nijar, da nufin su tattauna yadda za a shawo kan matsalar da ta afku, tun bayan hamɓarar da Gwamnatin Mohammed Bazoum.”
Baya ga jagoran tawagar, Abdulsalam Abubakar, Sarkin Sa’ad Abubakar III da kuma Omar Touray.
A ranar Alhamis ce dai ECOWAS ta nemi sojojin mulkin Nijar su yi gaggawar sauka, tare da maida mulki a hannun Bazoum a cikin kwanaki bakwai.
Sannan kuma ta ƙaƙaba takunkumi kan Nijar, wanda tuni ya fara aiki, inda Najeriya ta katse wutar lantarkin da ta ke bai wa Nijar.
Haka kuma Shugaban ECOWAS Bola Tinubu ya aika da wata tawagar domin ta tattauna da shugabannin Libya da Algeriya, ƙasashe biyu da su ma su ka yi iyaka da Nijar.
Tinubu ya umarci tawagar guda biyu su tattauna da dukkan masu ruwa da tsaki a Nijar, Libya da Algeriya, domin a samu a magance matsalar Nijar a cikin lumana, ba tare da an kai ruwa rana ba.
“Mu abin da ya fi damun mu shi ne ɗorewar dimokraɗiyya da kuma zaman lafiya a ECOWAS.”
Abubakar ya ce za su gana da shugabannin mulkin Nijar domin a samu mafita a cikin ruwan sanyi.
Sannan kuma ya ce ya na da yaƙinin tawagar sa za ta yi nasara.
A farkon wannan makon sai da ECOWAS ta tura Shugaban Chadi, ya je ya gana Shugabannin Mulkin Sojan Nijar.
Discussion about this post