‘Yan ta’adda na shirin kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna domin yin garkuwa da fasinjoji, kamar yadda hukumar tsaro na sirri ta rubuta a cikin wata wasika da aka aike wa Manajan Daraktan Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC).
A cikin wasikar mai dauke da kwanan watan 11 ga watan Agusta, hukumar SSS ta ce bayanan sirrin da ta samu na nuni da wata barazana da ke shirin yi wa zirga-zirgar jiragen kasa da tasowa daga Abuja zuwa Kaduna (AKTS) nan ba da dadewa ba.
Ya yi gargadin cewa “Gamayyar kungiyoyin ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga” na shirin kai hari kan jirgin “kowane lokaci daga yanzu.” Hukumar SSS ta ce harin na da nufin yin garkuwa da fasinjojin da ke cikin jirgin ne domin neman kudin fansa.
A dalilin haka SSS na kira ga hukumar NRC da ta tsaurara matakan tsaro a wannan layin dogo.
Daga cikin shawarar da hukumar ta ba NRC sun hada da, kara shawagin jirgin yaki a yayin da jirgin kasan ya kwashi fasinjoji. A kara saka jami’an tsaro a layin dogon sannan a saka shingayen sojoji a hanyoyin dake kusa da titin jirgin.
Sannan kuma sojoji su shiga dazukan da ke kewaye da kauyukan Byazhin, Jibi, da Ija domin ragargazar ‘yan ta’adda da ke boye a wadannan wurare.
Discussion about this post