Sanata Aliyu Wamakko dake wakiltar shiyar Sokoto ta Arewa a jami’yyar APC, a ranar Laraba ya yi juyayi da alhinin kisan kiyashin da ‘yan bindiga suka yi a wasu kauyukan dake karamar hukumar Tangaza.
A wani takarda da ke dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Wamakko ya aika da sakon ta’aziyar sa ga mazauna karamar hukumar da suka rasa yan uwan su a wannan harin.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ta rawaito cewa a ranar Asabar din da ta gabata wasu mahara da ake zargin ‘yan bindiga ne sun Kai wa kauyuka shida hari a karamar hukumar Tangaza.
Akalla mutum 30 sun mutu sannan mutane da dama sun ji rauni a dalilin harin.
Wamakko ya bayyana harin a matsayin abin takaici da rashin tsoron Allah.
“Kamata ya yi gwamnati ta dauki tsauraran matakai domin ganin ta hukunta duk wadanda ke da hannu a harin.
“Ina yi wa mazaunan karamar hukumar Tangaza jaje da ta’aziyar Allah ya gafarta wa wadanda suka riga mu gidan gaskiya ya sa AlJannatul Firdausi ta zama makoma.
Sanatan ya kuma yi wa matanen da suka ji rauni addu’ar Allah ya basu lafiya, Amin.
Discussion about this post