Farashin abinci, kudin mota da sauran ababen more rayuwa sun kara tsada bayan gwamnati ta cire tallafin man fetur a makon da ya gabata.
A ranar Litini din makon da ya gabata ne dogayen layukan man fetur suka dawo Najeriya bayan sa’o’i da Shugaban kasa ya sanar da cire tallafin man fetur.
Idan ba a manta ba a jawabin da ya yi bayan an rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayu a filin Eagle Square ne Shugaban kasa Bola Tinubu ya sanar cewa gwamnati za ta cire tallafin man fetur.
“ Yayin da muke yaba kokarin da gwamnatin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi wajen ci gaba da amfani da tallafin mai wannan gwamnati za ta cire tallafin mai.
“ Gwamnati za ta yi amfani da kudaden da take biya tallafin a baya wajen inganta ababen more rayuwa da suka hada da kiwon lafiya, ilimin da dai sauran su.
Jihar Legas
Zuwa yanzu farashin lita daya na man fetur a jihar Legas ya Kai Naira 700.
Wani dan Keke mai suna Rashidi Lawal dake daukan fasinja daga Iyana-Iba zuwa Mile 2 ya ce ya kan siya man naira 12,000 kullum idan ya fito aiki yanzu.
“Idan na siya man naira 12,000 na kan samu naira 20,000 sannan idan na biya ‘yan jagaliya kudi na kan samu naira 10,000 da zan je gida da su.
Lawal ya ce farashin kudin mota ya karu a jihar washe garin da gwamnati ta cire tallafin mai.
Ya ce kafin a cire tallafin mai daga Iyana-Iba zuwa Mile 2 a Keke naira 200 ne ake biya amma yanzu kudin ya Kai Naira 300.
“Ga dukan alamu farashin zai koma zuwa Naira 400 saboda kafin a cire tallafin man man naira 7,000 ne muke amfani da shi kulun rana amma yanzu man naira 7000 ya yi kadan.
Babban Birnin Tarayya Abuja
A Abuja mutane da dama na bayyana rashin jin dadin su ga yadda farashin man fetur ya zama yanzu.
Wakiliyar PREMIUM TIMES ta gano cewa daga Wuse Zone 2 zuwa kasuwan Wuse da ake biyan Naira 300 yanzu ya zama 600 sannan zuwa Aco Estate, tashar jiragen sama da secretariat ya zama naira 500 daga naira 250.
Sannan masu shiga motocin haya na Uber sun ce daga Wuse Zone 2 zuwa Wuye ko Wuse 2 da ake biyan Naira 700 zuwa 800 yanzu ya koma 1,500 zuwa 1,700.
Wani mai siyar da kayan lanbu Alimodu Yusuf ya ce zai rika siyar da yankan kankanan ko abarba akan naira 300 a mai maimakon 200 domin ya samu kudin ciyar da iyalinsa.
A kasuwar Wuse farashin kayan Miya bai tashi ba amma kilo daya na naman akuya ya tashi daga naira 3,200 zuwa 3700.
Wata mai siyan bijimin sa ta raba da mutane Ezehi Grace ta ce farashin bijimin sa ya tashi daga 345,000 zuwa 400,000 har zuwa 420,000.
Jihar Kano
A jihar Kano Wani tela mai suna Nazifi Muhammad dake Fagge ya ce tun da Mai ya kara kudi ya kasa siyan man fetur ya zuba a janaretansa domin ya yi dinkin.
“Ni dai na hakura na koma ga yin addu’o’i Allah ya yaye mana wannan matsala da muka shiga.
Wani mai zuwa jihar Legas da Abia siyo takalma ya ce takalmi ya karu daga Naira 3,500 zuwa 6,000 sannan kudin mota ya karu daga 13,000 zuwa 18,000.
Farashin kudin mota daga jihar Kano zuwa wasu jihohin ya karu kamar haka; daga Abuja zuwa Kano ya karu daga N3,500 zuwa N5,000, Borno daga N4,000 zuwa N5,500, Adamawa 5,000 zuwa N7,000, Taraba N6,000 zuwa N8,000, Gombe N3,000 zuwa N4,500, Bauchi N2000 zuwa N3,000, Niger N4,000 zuwa N5,500, Benue N7000 zuwa N8,000 da Nasarawa N5,000 zuwa N7,000.
Jihar Katsina
Karin farashin man fetur ya shafi harkokin kasuwanci a jihar.
Hukumar sufuri ta jihar KSTA ba ta kara kudin mota ba amma sauran ababen hawa na haya sun kara farashi zuwa Naira 1,000.
Zuwa yanzu daga Katsina zuwa Gusau jihar Zamfara ya karu daga 3,000 zuwa 4,000.
Daga Dutsen Ma ya karu daga 500 zuwa 900 sannan daga Katsina zuwa Kano ya karu daga Naira 1,500 zuwa 2500.
Jihohin Ribas, Ekiti, Enugu duk na kukan tsadar farashin kaya da suke fama da shi a dalilin Karin farashin mai.
Discussion about this post