Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya maida wa tsohon gwamna Abdullahi Ganduje martani, cewa zautuwa ce ya yi da ruɗewa amma marin da ya ce zai gaura masa ba na mai natsuwa bane.
Idan ba a manta ba Ganduje ya bayyana wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa da zai hada ido da Kwankwaso da ya gaura masa mari.
A tattaunawa da Kwankwaso ya yi manema labarai ya ce Ganduje ya ruɗe ne, amma marin sa ba a nan kusa ba.
” Dukkan su yara na ne a siyasa, amma in ba ruɗewa ba, ya ya zai ganni wai har ya mare ni. Ganduje fa mun zauna da shi lafiya a siyasance na tsawon lokaci amma abubuwa suka taɓarɓare a tsakanin mu saboda son zuciya.
Da ya ke magana kan rushe-rushen da ake yi a Kano, Kwankwaso ya ce ba tun yanzu ba gwamnatin NNPP ke gargaɗin mutane kada su sayi filaye da gidajen gwamnati da Ganduje ya saida wa kansa da ƴaƴan sa.
” Duka inda gwamnati ta ke rusawa, wurare ne da Ganduje da maƙarraban sa suka saida wa kan su da aminan su. Kuma filaye ne na gwamnati suka yi karfa-karfan su.
Discussion about this post