Dan majalisan dake wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisar Tarayya, kuma dan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, Bello El-Rufai ya ce gwamnan Kaduna Uba Sani ne yayi tsayin daka wajen ganin ya yi nasara a zaben dan majalisar Kaduna ta Arewa da yayi a zaben 2023.
A hira da yayi da talbijin din Channels ranar Laraba Bello El-Rufai ya ce gwamnan Kaduna Sanata Uba Sani ne kan gaba wajen saka shi tun farko ya amince ma ya fito takarar kujerar dan majalisar.
” Mahaifina El-Rufai bai ce min Uffan ba game da takarata. Gwamnan Kaduna Sanata Uba Sani ne ya shawarce ni tun farko sannan ya yi ruwa yayi tsaki Allah ya bani nasara a zaben kujerar mamban Kaduna Ta Arewa. Wasu na ganin kamar don ina dan gwamna a lokacin, shikenan mahaifina zai mara min baya. Ba haka abin yake ba.
” Ni mahaifina ma bai saka bakin shi a harkar siyasa ta ba, illa addu’a da ya yi min da fatan Alkhairi, amma idan so samunsa ne ma ba zai so in fito takara ba.
Bello ya kara da cewa ko da ya fito takara, akwai abubuwa da dama da ya lura mutanen yankin na matukar fama da su, da suka hada da ababen more rayuwa. Wadannan abubuwa sune ya maida hankali akai tun a lokacin da yake neman kuri’a.
” Kuma zan ci gaba yi wa mutane aiki tukuru domin jindadin su.
” Tun kafin in shiga majalisa, yanzu haka mun tsara wasu kudirori har 10 domin mutanen mu. sannan a haka tuni har na fara baiwa yara tallafin karatu da dama dake karkashin yankin da na ke wakilta.
Discussion about this post