Sanata Abdul Ningi daga jihar Bauchi na jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa akalla sanatoci 67 ne ke marawa AbdulAziz Yari baya ya zama shugaban majalisar dattawa.
Ningi ya kara da cewa, yana da yakinin Yari zai yi shugabanci mai nagarta idan ya zama shugaban majalisar dattawa, saboda kwarewarsa.
” Shine ya sa muke tare da shi Yari, babu wanda zai ce ya san komai ko ya fi kowa iyawa a majalisar dattawan da na wakilai.
” Yana bukatar gogaggu, tsoffin hannu irin mu su nuna masa hanya.
Daga nan sai ya yi kira ga jam’iyyar APC mai mulki ta bari ‘ya’yan ta su zabi shugabannin da suke so ba tare da an yi musu katsalandan.
Sannan kuma Sanata Sani Musa, Orji Kalu da Osita Izunaso duk suna nan ana ci gaba da tattaunawa da su.
Hakanan shima sanata Samaila Kaila na APC ya ce Yari ya ke yi, amma kuma duk wanda ya samu a karshe za su mara masa baya domin nasarar mulkin Tinubu.
Dalilin da ya sa nake neman zama shugaban majalisar Dattawa -Yari
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari ya bayyana cewa dalilin da ya sa yake neman zama shugaban majalisar Dattawa saboda kawo ingantaccen mulki mai nagarta a majalisar ne.
Ya bayyana haka da yake hira da manema labarai cewa tabbas yana da kwarewar da zai iya shugabantar majalisar dattawa, idan ya zama ba za a yi dana sani ba.
Discussion about this post