Hukumar Raba Tallafin Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP), ta yi gargaɗin cewa sama da mutum miliyan 25 ka iya afkawa cikin barazanar matsananciyar yunwa tsakanin Juni zuwa Agusta na wannan shekara.
Wannan kintace da hasashe dai Daraktan WFP da ke Najeriya, David Stevenson ne ya sanar da shi, a lokacin da ya ke ƙaddamar da Tsare-tsaren Shirin Bayar da Agaji ga Najeriya (CSP), ranar Laraba, a Abuja.
“Yayin da matsalar abinci ke ƙara yawaita saboda matsalar tsaro da sauran dalilai, akwai yiwuwar fiye da mutum miliyan 25 za su yi fama da yunwa tsakanin watannin Yuni zuwa ƙarshen Agusta na 2023,” cewar Stevenson a jawabin sa.
Wannan lokaci shi ne lokacin shuka ko dashen shuka zuwa lokacin girbi, lokutan da ayyukan samun kuɗaɗen sayen abinci ga marasa galihu ke ƙaranci sosai.
Jami’in ya ce jihohin Barno, Adamawa da Yobe kaɗai ya a samu mutum miliyan 4.4 da za su fuskanci yunwa a cikin watannin huɗu.
Sannan kuma ya ce a yankin Arewa maso Gabas kaɗai za a samu ƙananan yara kamar miliyan biyu da za su yi fama da rashin abinci mai gina jiki.
Ya ce duk da wannan matsala da ake ganin tunkarowar ta, WFP ta na kan tallafa wa mutum miliyan 2.1 a Najeriya, cikin 2023.
Ya ce su na yin tallafin ta hanyar bayar da abinci, kayan abinci masu gina jiki, tallafin kuɗaɗe da kuma ayyukan sake gina al’ummar da rikice-rinkice ya tarwatsa.
Ya ce Shirin CSP na ƙoƙarin shawo kan matsalar yunwa a Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da kuma haɗa guiwa sa shirin SDGs domin bunƙasa ayyukan jinƙai a faɗin ƙasar nan.
Ya ce “shirin ya shirya kashe dala miliyan 56 a Najeriya domin ganin an shawo kan yunwa daga nan zuwa 2030, kamar yadda Shirin SDG Zango na 2 ya tanadar,” cewar sa.
Discussion about this post