Kungiyar G7 da ke adawa da zaɓin Tajuddeen Abbas a matsayin wanda jam’iyyar APC ta zaɓa ya don ya zama kakakin majalisar wakilai ta bayyana cewa ta nan kan bakanta cewa ba za su amince da zaɓin Tinubu da APC ba wajen kakakin majalisa.
Kungiyar da ya kunshi mataimakin kakakin majalisa, Idris Wase, sai kuma Yusuf Gagdi, Mukhtar Betara, Sada Soli, Aminu Jaji da Mariam Onouha sun yi ganawa a Otel ɗin Transcorp dake Abuja ranar Asabar.
Bayan taron, Soli ya bayyana wa manema labarai cewa ba za su bi zaɓin jam’iyyar su ta APC ba.
” A cikin wannan mako da da zamu shiga za mu sanar da ɗan takarar da dukkan mu da magoya za mu mara wa baya, amma ba za mu bi wanda Tinubu, da APC suka ƙaƙaba mana ba.
Shima Gagdi ya yi ƙarin haske akan abinda suka tattauna a wurin ganawar. Gagdi ya ce ” Za mu bayyana sunayen wadanda mu ke so su zama kakakin majalisa da mataimakin. Ba zamu sa ido muna gani a yi mana ƙarfa-ƙarfa akan abinda ba haka ba.
Idan ba a manta ba jam’iyyar APC ta zaɓi Tajuddeen Abbas daga Jihar Kaduna a matsayin zaɓin ta ya shugabanci majalisar wakilai.
Sai dai tun bayar sanar da haka wasu gaggan ƴan majalisa suka yi hannun riga da jam’iyyar.
Discussion about this post