Gwamna Darius Ishaku na Jihar Taraba, ya rattaba hannun amincewa a kamfaci naira biliyan 2 domin a sayo masa motoci, shi da matar sa, mataimakin sa da kuma matar mataimakin na sa.
Za a kamfaci kuɗaɗen a sayo masu motocin bankwana da talakawan jihar, makonni biyu kafin fitar su daga gidan gwamnatin Taraba.
Ishaku da mataimakin sa za su kammala wa’adin su na shekara takwas kan mulki a ranar 29 Ga Mayu.
Za a sayo wa Gwamna Land Cruiser Toyota SUV guda biyu, Toyota Hilux biyu wadda jami’an tsaron sa za su riƙa yi masa rakiya a cikin ta, sai kuma wata rangaɗeɗiyar mota ɗaya.
Ita kuwa matar Gwamna za a sayo mata Toyota Land Cruiser SUV ɗaya da motar jami’an tsaro ɗaya.
An amince a cire kuɗin a sayo motocin a Taron Majalisar Zartaswa ta Jihar na Ƙarshe, wanda shi Gwamna Darus Ishaku ya jagoranta.
Majiya ta ce a wurin taron an ce tunda dai tun bayan hawan Darus gwamna da tsoffin motocin da ya gada a 2015 ya riƙa amfani har yanzu, shi da mataimakin sa, saboda haka ya cancanci a sai masu sabbin motocin zirga-zirgar su ta yau da kullum bayan sun sauka daga mulki.
Darus da matar sa za su tashi da motocin naira biliyan 1.3, shi kuma mataimakin sa da matar sa motocin Naira miliyan 750.
Mataimakin sa Haruna Manu zai samu Land Cruiser SUV ƙaramin giredi biyu, sai motar jami’an tsaro ɗaya, sai kuma ita ma matar sa SUV ɗaya da rangaɗeɗiyar mota ɗaya.
Wakilin mu ya tuntuɓi Kwamishinan Yaɗa Labarai na Taraba, Lois Emmanuel, amma bai yi magana ba.
“Ba na cikin jihar, na yi tafiya.” Cewar sa.
Discussion about this post