Kotun shari’a a jihar Kaduna ta umarci wata matan aure mai suna Fatima Muhammad da ta biya mijinta naira 80,000 kudin sadakin auren da ya biya a kanta.
Alkalin kotun Malam Muhammad Adamu-Shehu ya yanke wannan hukunci ne bayan Fatima ta shigar da kara kotu ta na so a raba auren ta da mijin ta.
Ita dai Fatima ta ce ta gaji da auren ne kawai. Ba ta kaunar mijinta kwatakwata, shine ta ga abinda yafi dace wa shine kawai su rabu kowa ya kama gaban sa.
Sannan kuma ta ce naira 80,000 din da mijin ya biya sadakin ta, za ta maida masa da su. Amma kuma ta roki kotu ta bata ikon rike ƴar su guda.
Lauyan dake kare mijin Fatima L.R Ibrahim ya ce mijin Fatima ya ce a fadi wa kotu cewa har yanzu yana son matarsa sosai, yana rokon kotu ta bashi dama su sasanta kan su, domin shi fa haryanzu yana matuƙar kaunar matan sa.
Discussion about this post