Shugaban Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Najeriya (MACBAN), ya yi alƙawarin cewa za su bada haɗin kai domin tabbatar da cewa babu wani makiyayin da zai karakaina da shanu cikin Abuja, a ranar Litinin, ranar rantsar da Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu.
Wannan sanarwa ta fito ne daga cikin wata sanarwar da Mataimakin Daraktan Hukumar Tsaftace Muhallin Abuja (AEPB), Janet Peni ta fitar a ranar Laraba, a Abuja.
Ta ruwaito Shugaban Miyetti Allah, Usman Muhammad ya na cewa, “za mu taimaka domin mu tabbatar cewa babu wani makiyayin da zai yi kiwo a cikin babban birnin tarayya, Abuja a ranar 29 Ga Mayu, ranar rantsar da Tinubu.
“Ɗabi’ar mu ce karɓar baƙi a tsaftataccen Muhalli, don haka gwamnati mai hawa babbar bakuwar mu ce, za mu karɓe ta hannu bi-biyu.”
Ya ce idan an tuna, sun yi ganawa da Ministan Abuja, Mohammed Bello, inda su ka tattauna buƙatar wasu masu zuba jari daga Dubai za su zo Abuja, domin su inganta dabarun kiwon shanu a yankin FCT, ta yadda za a ci ribar abin sosai.
Shi ma Shugaban Miyetti Allah na Gundumar AMAC, Adamu Rabo, ya yi alƙawarin yin bakin ƙoƙarin ɗaukar wannan matakin hana karakainar makiyaya a Abuja lokacin rantsuwa da muhimmanci sosai.
Discussion about this post