Babban Daraktan Ofishin Tsare-tsaren Kasafin Kuɗaɗe, Ben Akabueze, ya ce aƙalla Najeriya na buƙatar ta riƙa kashe dala biliyan 100 duk shekara, idan ana so a cimma samar da dukkan ayyukan raya ƙasa da ake tsananin buƙata.
Akabueze ya ce tilas an fa an raba ƙafa wajen kashe kuɗaɗen, wato gwamnati da kuma masu kamfanoni da masana’antu na kan su riƙa zuba kuɗaɗe wajen gudanar da ayyukan ci gaban da ƙasar nan.
Ya bayyana haka a ranar Laraba, a wurin taron nuna wa zaɓaɓɓun ‘yan majalisar tarayya sanin makamar aikin majalisa.
Ya ce kama daga Gwamnatin Tarayya da gwamnatin jihohi sun kasa iya kashe dala biliyan 100 wajen bunƙasa ayyukan raya ƙasa a duk shekara.
“Na farko dai kafin a iya saisaita tattalin arzikin Najeriya, mu na buƙatar a riƙa kashe dala biliyan 100, aƙalla duk shekara.
Ya ce kasafin da ake samu daga gwamnatin tarayya a duk shekara bai wuce dala biliyan 30 ba. Jihohi da Babban Birnin Tarayya, FCT ba su ƙara wa kasafin Najeriya wani karsashi ko ƙarfi. Wato idan ma sun kashe dukkan kuɗaɗen da tarayya ke ba su, har yanzu dai ana barin giɓi sosai,” haka Akabueze ya bayyana.
Babban Daraktan na kasafin kuɗaɗe, ya nuna matuƙar damuwa ganin babu wata ƙwaƙƙwarar doka kan kasafin kuɗaɗe.
Sai dai ya ce akwai ƙudiri ajiye a Majalisar Tarayya. Daga nan ya yi kira ga majalisa mai barin gado su ƙoƙarta su saka hannu kan ƙudirin domin ya zama doka.
Discussion about this post