Ƴan sandan babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja sun tabbatar da mutuwar mutum ɗaya a wani rikici da ya ɓarke a unguwar Gwarimpa ranar Litinin.
Kakakin rundunar ma Abuja SP Josephine Ade ta faɗa wa BBC Hausa cewa rikicin ya ɓarke tsakanin wasu ƙabilu guda biyu mazauna wani yanki da ake kira Gwarimpa village, wato Ƙauyen Gwarimpa.
Bayanai sun ce tun ranar Asabar ne tarzomar ta fara bayan ƙabilar Gbagyi sun yi yunƙurin korar wasu da suke zargin suna dillancin ƙwayoyi a yankin da yake kawo ruɗani tsakanin mutanen ƙauyen.
Ƴan sanda sun ce mutumin da aka kashe matashi ɗan shekara 20, kuma ya rasu ne sanadin raunukan da aka ji masa tun a jiya Lahadi.
Sun ce rikicin ya sake ɓarkewa da safiyar Litinin, bayan Hausawa sun samu labarin rasuwar ɗan’uwan su da aka kai asibiti sanadin raunukan da ya ji, ko da yake sun yi ƙoƙari, a cewar Josephine sun shawo kan lamarin.
Ta ce ba gaskiya ba ne jita-jitar da ake yaɗawa cewa Fulani makiyaya ne suka kai hari unguwar Gwarimpa a cikin birnin Abuja.
Wasu kafofin yaɗa labarai sun ba da rahoton cewa faɗan ƙabilancin ya yi sanadin mutuwar mutum uku, zargin da Ade ta ce babu ƙanshin gaskiya a ciki.