Ƙungiyar Tsoffin ‘Yan Majalisar Wakilai ta Ƙasa daga ɓangarorin ƙasar nan na shiyyoyi shida, sun amince da cewa Muktar Betara daga Jihar Barno ne ya fi cancanta ya zama Kakakin Majalisar Tarayya Zango na 10.
Sun nuna wannan zaɓi da amincewa da Betara a cikin wata takardar bayan taro da su ka fitar, bayan kammala taron su a ranar Juma’a, a Abuja.
Mambobin dai sun haɗa da na zango na 6, na 7 da na 8. Haka kuma a cikin su, akwai mambobin da ke kan kujera a yanzu haka, amma kuma ba su samu nasarar sake komawa majalisa ba a zaɓen 2023.
Cikin waɗanda su ka sa hannu kan takardar bayan taron, har da Emeka Anohu, daga jihar Anambra da Golu Timothy daga Jihar Filato.
Dukkan su biyu ɗin sun yi majalisa ne a zango na 8. Sauran sun haɗa da Mohammed Almakura daga Nasarawa, Nado Karibo daga Bayelsa, Bashir Babale daga Kano, Segun Odebumi daga Oyo da sauran su.
Betara dai ya na wakiltar Ƙananan Hukumomin Biu/Bayo/Shanu/Kwaya Kusar daga Jihar Barno.
Sun ce ya cancanta, mutum ne kamili, wanda ya cancanta, mai haɗa kan jama’a kuma mai tsoron Allah.
Sai dai kuma a wani labarin daban, wasu ‘Yan Majalisa da ke kan kujera a yanzu, kuma sun ci zaɓen ci gaba a zangon 2023 zuwa 2027, sun yi fatali da tsarin karɓa-karɓar da Gwamnonin APC su ke so a bi wajen zaɓen shugabanni.
Wasu mambobin Majalisar Wakilai ta Tarayya sun soki tsarin karɓa-karɓar da Gwamnonin APC ke so a bi wajen zaɓen Shugabannin Majalisar Dattawa da na Tarayya Zango na 10.
A wata tattaunawa da aka yi da Akin Alabi, ɗan APC daga Oyo da kuma Rolland Igbakpa, ɗan PDP daga Delta, sun ce zai yi wahalar gaske bayar da manyan muƙaman majalisar dattawa da ta tarayya ga yankunan Arewa, bisa la’akari da cewa Bola Tinubu da Kashim Shettima sun ci zaɓe a ƙarƙashin tikitin Muslim-Muslim.
Da ake tattaunawa da su a shafin Tiwita ɗin PREMIUM TIMES dangane da yadda Majalisar Tarayya Zango na 10 Za Ta Kasance, sun ce amma dai maganar gaskiya idan aka dubi yadda aka yi Muslim-Muslim a APC, kuma sannan aka yi la’akari da wasu batutuwa na siyasa, to maganar a bayar da masu manyan muƙamai ga Arewa bai ma taso ba.