Sashen Kula da Yawan Jama’a na Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), ya tabbatar da cewa nan da ƙarshen Afrilu, wato kwanaki biyar masu zuwa, yawan jama’ar da ke ƙasar Indiya zai fi yawan mutanen Chana.
Daraktan sashen na mai suna John Wilmoth ya bayyana haka a wurin taron manema labarai a ranar Litinin, a Hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke birnin New York na Amurka.
Wilmoth ya ce babban abin da ya haifar da Indiya za ta fi kowace ƙasa jama’a nan da ‘yan kwanaki kaɗan, shi ne saboda yawan haihuwar da ake yi a Indiya ya na ƙaruwa sosai, yayin da kuma yawan haihuwar ƙara raguwa sosai a Chana.
Adadin yawan jama’ar ƙasashen biyu dai ya kai kashi 1 bisa 3 na adadin yawan mutanen duniya arankatakaf, wato biliyan 8.
” Zuwa ƙarshen Afrilu yawan mutanen Indiya za su kai biliyan 1 da miliyan 425 da dubu 775 da ɗari 850.
” Adadin zai kasance ya fi na Chana yawa da kaɗan, wadda ita yawan na ta mutanen kaɗan su ka haura biliyan 1.4 a ƙarshen 2022.
” Yawan al’ummar ƙasar Chana ya kai ƙololuwar da ya kai malejin da daga nan kuma ya koma ya na raguwa a cikin 2023.
“Haka nan kuma an ƙiyasta cewa adadin mutanen Sin zau ragu sosai zuwa ƙasa da biliyan ɗaya.” Inji daraktan.
A baya cikin shekarar 1971, ƙasashen biyu su na kankankan a matakin haihuwa.
Amma a zuwa shekarun 1970s sai ƙarfin yawan haihuwa a Chana ya ragu da rabi.
” Zuwa ƙarshen 2022 yawan haihuwa ya ragu sosai a ƙasar Chana.
“Cikin shekarun 1980s Chana ta shigo da tsarin haihuwar yaro ɗaya ga ma’aurata. Amma an soke tsarin a cikin 2016. A daidai wancan lokacin kuma yawan haihuwa na ƙaruwa a Indiya.
Wilmoth ya ce akwai hasashen yawan dattawa zai ƙaru sosai a Chana.
Discussion about this post